Latest
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa watau EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumarsa na sane ta bari tsarin sauya naira ke tafiya babu ƙame.
Kotun koli a Najeriya ya bukaci a yi gyara a kudin tsarin mulkin kasar nan saboda wasu dalilai da ka iya zama barazana ga yadda ake tafiyar da lamura a kasar.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki masu neman zama shugaban kasa, gwamna, da sauran mukaman siyasa su amince da duk abinda INEC ta sanar bayan zaɓe .
Jam’iyyun adawa guda biyar a jihar Oyo sun nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu kwanaki uku kafin babban zabe.
Rundunar yan sanda reshen jihar Legas ta ce wasu fusatattun kwastomomin banki sun cinna wa naurar ATM wuta sakamakon rashin kuɗi amma komai ya dawo daidai.
Yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun siyasa daban-daban a Najeriya sun hadu a babban birnin tarayya domin rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya
Za a ji wasu Kungiyoyin Magoya Bayan Buhari/Osinbajo su na goyon bayan Atiku Abubakar. A zaben da za ayi, kungiyar ta ce tana harin nasarar Atiku/Okowa a 2023.
Majalisar tsaro a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu, ta bayar da umurnin gudanar da babban zaben shugaban kasa da na yan majalisa a ranar Asabar mai zuwa.
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa manyan Sakatarori 12 a gwamnatin Kano yayin da ya rage watanni ya bar mulki bayan zaben watan Maris.
Masu zafi
Samu kari