Gwamna Ganduje Ya Kara Nada Sabbin Manyan Sakatarori 12 a Kano

Gwamna Ganduje Ya Kara Nada Sabbin Manyan Sakatarori 12 a Kano

  • Gwamnan Kano ya zabo wasu mutane 12, ya naɗa su mukamin babban Sakatare a gwamnatinsa
  • Bayanai sun nuna cewa da yawansu suna rike da wasu mukamai gabanin samun wannan sabon matsayi
  • A wata sanarwa da Sakataren watsa labaran gwamnan ya fitar, ya ce za'a rantsar da su gobe Alhamis da karfe 2:00 na rana

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa sabbin manyan Sakatarori 12 a wani bangare na yunkurin sauke hakkin al'umma.

Jaridar Punch ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na ofishin gwamna, Abba Anwar, ya fitar ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu, 2023.

Abdullahi Ganduje.
Gwamna Ganduje Ya Kara Nada Sabbin Manyan Sakatarori 12 a Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Jerin sunayen waɗanda Ganduje ya naɗa

Mutanen da gwamna ya naɗa sun haɗa da, Masur Yakubu, wanda kafin yanzu shi ne Darakta a ma'aikatar ayyuka, Salisu Ɗan Azumi, Darakta daga ma'aikatar kananan hukumomi da Dakta Sa’adatu Sa’idu Bala daga ma'aikatar lafiya.

Kara karanta wannan

Adamu da Gwamnoni 4 Sun Gana da Ministan Buhari Kan Sauya Naira, Sabbin Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran sun ƙunshi, Ahmad Tijjani Abdullahi, babban Sakataren hukumar kimiyya da fasaha; Baba Sharu Dala, darakta daga ma'aikatar yaƙi da cin hanci, da kuma Aliyu Yakubu Garo daga ma'aikatar wuraren tarihi.

Abbas Sanusi, Dakta Tijjani Hussain, Yahaya Nuhu Amasaye, Aisha Abba Kailani, Mustapha Madaki Huguma, da kuma Musa Tanko Garko, duk suna cikin waɗanda Ganduje ya naɗa mukamin babban Sakatare.

Mafi yawan mutanen da aka naɗa manyan Sakatarorin suna rike da wasu muƙamai a wasu hukumomi ko ma'aikatu daban-daban a jihar Kano.

A cewar sanarwan, dukkan waɗanda aka naɗa a sabbin guraben gwamnatin zasu fara aiki nan take.

PM News ta rahoton Sanarwan na cewa:

"Baki ɗaya wadanda aka baiwa mukamin babban Sakatare sun taba nuna kwarewarsu a harkokin gwamnati, muna da yakinin zasu iya bayan bin matakan tantancewa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Kutsa Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10, Bayanai Sun Fito

"Na umarci su yi aiki da mutanen da ke karkashinsu a kowane wuri aka tura su, dole su fifita haɗin kai wajen sauke nauyin dake kansu."

Legit.ng Hausa ta gano cewa a gobe Alhamis za'a gudanar da bikin rantsar da sabbin Sakatarorin a Coronation Hall da ke fadar gwamnatin Kano da misalin karfe 2:00 na rana.

Atiku Ya Kara Caccakar Gwamna Wike

A wani labarin Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP ya kalubalanci gwamna Wike ya fito ya faɗi wanda yake goyon baya kai tsaye

Ta bakin mai magana da yawunsa, Wazirin Adamawa ya ce Wike ba shi da zarrar da zai iya faɗa wa mazauna Ribas su zabi jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel