Latest
Mambobin ƙungiyar ma'aikatan majalisar dokoki ta Najeriya reshen jihar Kano sun rufe zauren majalisa yayin da suka fara yajin aikin sai baba ta gani ranar Litinin.
Majalisar zartarwa karkashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta amince da ƙara zunzurutun kudi N2.18tr a kasafin kuɗin shekarar 2023 da ke daba da ƙarewa.
Yayin da ake ta rigimar tsige gwamna Siminalayi Fubara, mambobi masu goyon bayan mai girma gwamna sun zabi Ehie Edison a matsayin sabon shugaban majalisa.
NLC ta yi bayanin abin da ya sa ba za ta shiga duk taro da Simon Lalong zai halarta ba, ta ce taron da za ayi da gwamnatin tarayya, Ministan ba zai shiga ciki ba.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya ankarar da cewa idan ba a yi da gaske ba dangane da Boko Haram, zata iya shafe Najeriya daga taswira.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benuwai, Raymond Erukaa, ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane inji ɗansa.
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya kalubalanci yadda shugaban majalisar, Godswill Akpabio ke jagorantar majalisar cikin rashin kwarewa, ya ce ya fishi kwarewa.
Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a wasu ƙauyukan jihar Benue guda biyu. Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum bakwai.
Atiku Abubakar, wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya zargi kotun koli da halasta haram da kuma kirkirar takardan bogi yayin hukuncin kotun.
Masu zafi
Samu kari