Latest
Sherif Lawal ya fafata ne a filin dambe na J Hackney Leisure inda ya ji rauni a zagaye na hudu a karawarsa da Malam Varela; an tabbatar da mutuwarsa a asibiti.
Dan Majalisar Tarayya da ke wakilta Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai ya magantu kan yadda suke da Gwamna Uba Sani inda ya ce har yanzu mai gidansa ne.
'Yan bindigar sun kai hari kauyen Benue inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, tare da kashe mutane 11 ciki har da wata mata mai dauke da juna biyu.
Dalibar da aka ci zarfi a makarantar Lead British International School, Namitra Bwala ta shigar da kara kotu tana neman a bita ta diyyar N500,000, 000.
Babban dan Mamman Nur, wanda ya kafa kungiyar ta'addanci ta ISWAP, Mahmud Mamman Nur Albarnawy, ya mika wuya ga jami’an hukumar NSCDC a Maiduguri, jihar Borno.
Zaratan jami’an hisba a jihar Kano sun cafke wasu matasa guda 20 da ake zargi da aikata badala a wani gidan shakatawa dake titin ring road a jihar.
Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta samar da kwarya-kwaryan kasafi matukar za ta biya karin albashin ma’aikata da kungiyoyin kwadago ke ta fafutukar a yi.
Dakarun hukumar DSS sun shiga har cikin harabar kotu yayin da ake tsaka da shari'a, sun cafke mutum 2 da ake tuhuma duk da gargaɗin alkali a jihar Ogun.
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labor, Peter Obi ya bayyana dalilan da suka sa ya ziyarci Atiku Abubakar, Bukola Saraki da Sule Lamido.
Masu zafi
Samu kari