Latest
Gwamnatin tarayya ta kungiyoyin kwadago za su koma teburin tattaunawa domin sake duba kan batun mafi karancin albashi da yake ta yamutsa hazo a kasar nan.
Mambobi 12 na majalisar dokokin jihar Kano sun yi mubaya'a ga Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero yayin da suka kai masa ziyara a fadar Nasarawa jiya.
Rundunar ƴan sanda ta samu nasarar hallaka Auwalu Mahaukaci, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya damu al'umma a kewayen karamar hukumar Ɗandume a Katsina.
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya fayyace wa 'yan Najeriya dalilin rashin jawabin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ga majalisa kamar yadda aka ce zai yi.
Al'ummar Najeriya sun yi zafafan martani ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kirkiro sabon taken kasa a lokacin da rashin tsaro da hauhawar farashi suka addabi mutane.
Masu ruwada tsaki a shiyyar Kano ta Kudu sun buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gaggauta sauya tunani, ya mayar da sarakunan da ya tsige nan take.
Hukumar NAHCON a Najeriya ta ja kunnen mahajjata a kasar kan saɓa dokokon aikin hajji a Saudiya yayin da ake shirin koro wasu mahajjata da suka saba doka.
Wasu miyagun 'yan ta'adda sun kai farmaki cikin kasuwa a jihar Kaduna. 'Yan ta'addan sun hallaka mutum 12 yayin da suka raunata wasu mutane da dama.
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Legas ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazan jihar, Idris Oloshogbo, wanda ya rasu bayan dawowa daga Ɗawafi a Makkah.
Masu zafi
Samu kari