Latest
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a gwamnatin Muhammadu Buhari, Babachir Lawal ya soki salon mulkin Bola Tinubu inda ya ce hawansa ke da wuya komai ya lalace.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon shugaban INEC farfesa Attahiru Jega shugaban kwamitin gudanarwa a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.
Tun kafin a fara batun 2027, ana bakar adawa tsakanin Kwankwasiyya da mutanen Gandujiyya. A Kaduna, ana shuka irin rigima tsakanin Nasir El-Rufai da Uba Sani.
Gwamnonin Arewa maso yamma sun nemi taimakon majalisar dinkin duniya kan magance matsalolin tsaro, talauci, yaran da ba su zuwa makaranta da kiwon lafiya.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada shugabannin kwamitin gudanarwa da mambobinsu 555 a manyan makarantun Najeriya 111 a yau Asabar 18 ga watan Mayu.
Alhaji Aliko Dangote ya ce matatarsa za ta wadatar da Nahiyar Afirka da mai nan da watan Yuni da zamu shiga yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalar da mai.
Hukumar EFCC za ta binciki dan majalisa, Aminu Sani-Jaji bisa zargin taimakon yan bindiga domin ayyukan ta'addaci a kan cimma manufar siyasa a jihar Zamfara.
Ma'aikatar lafiya a jihar Kano ta bayyana cewa kimanin kaso 28.5 na wadanda ke da shekaru 30 zuwa 79 na dauke da cutar hawan jini. Cutar ka iya jawo ciwon koda.
Gwamnatin tarayya ta fara raba kayan tallafin noma ga manoma daga shiyyoyi uku na jihar Kano a wani yunkuri na habaka samar wa kasa abinci da habaka noma.
Masu zafi
Samu kari