2027: Rigima Ta Kaure tsakanin Musa Mai Sana'a da 'Yan Fim kan Tallata Tinubu
- An fara samun sabani a tsakanin 'yan wasan Kannywood kan tallata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027
- Musa Mai Sana'a ya fito ya yi kaca-kaca da masu sukar gwamnatin Shugaban Bola Tinubu, lamarin da ya kara daukar hankalin jarumai
- Aminu Saira, Sadiq Sani Sadiq na cikin 'yan wasan Hausa da suka fara caccakar salon mulkin Bola Tinubu domin hana shi tazarce
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tallata shugaban kasa Bola Tinubu domin samun tazarce a zaben 2027 ya fara jawo baraka a tsakanin 'yan fim a Arewacin Najeriya.
An fara samun sabani ne bayan jarumi Sadiq Sani Sadiq ya yi wani bidiyo yana sukar salon mulkin Bola Tinubu tare da kiran kar a sake zaben shi.

Source: Facebook
A wani bidyo da DCL Hausa ta wallafa a Facebook, Musa Mai Sana'a ya kare kan shi game da tallata jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Sadiq Sani Sadiq ya caccaki Bola Tinubu
Legit Hausa ta rahoto cewa jarumi Sadiq Sani Sadiq ya fito a wani bidiyo ya caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana kira ga jama'a da su kauracewa sake zaben shi.
Jarumin ya ce:
"Allah mun tuba wajen zaben wannan gwamnatin ta Tinubu. Mu kiyaye saboda karara ta nuna cewa ba masoyin al'ummar Arewa ba ne.
Ya ƙara da cewa:
"Ga kwatance nan, ka duba abubuwan da suke faru wa a jihar Zamfara, ka duba abubuwan da suke faruwa a jihar Katsina, ka duba abubuwan da suke faruwa a Kebbi, Sakoto, Neja, Kwara, Benue, Filato, Borno, Yobe, Gombe ga shi Borno na ta dauka."
Musa Mai Sana'a ya kare Tinubu
A na shi bangaren, Musa Mai Sana'a ya ce siyasa ra'ayi ne kuma ko uba da dan shi suna iya sabawa, ya ce bai kamata a ce Bola Tinubu bai tsinana komai ba.

Kara karanta wannan
Jarumi Sadiq Sani Sadiq ya fara ɗaukar hankalin ƴan ADC da ya nemi a canja Tinubu a 2027
Game da tallata Tinubu, Mai Sana'a ya ce idan lokaci ya yi, za su fadawa 'yan Najeriya abubuwan da Bola Tinubu ya yi wa 'yan kasa.
Ya kara da cewa suna aiki karkashin Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro domin wayar da kan jama'a game da matsalolin da ake fuskanta a fadin Najeriya.
Tinubu: An yi wa Mai Sana'a rubdugu
A martanin da ya yi a Facebook, jarumin Kannywood, Bello Muhammad Bello ya yi kakkausan martani ga Musa Mai Sana'a, inda ya ce:
"Kuskure ne babba mutum ya ɗauka cewa yunwa ko neman na abinci hujja ce..."
"Masana'antar mu tana buƙatar kariya daga masu son zuciya don neman na abinci. Muna nan daram a matsayin iyayen gida, kuma ba za mu zuba ido ana lalata kima da martabar da muka sadaukar da rayuwar mu a kai ba."
A na shi bangaren, Aminu Saira ya yi martani yana sukar gwamnatin Tinubu da masu tallata shi a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce:
"A saurari matakin farko da za mu fara da shi a watan Afrilu mai kamawa,"

Source: Facebook
Jam'iyyar ADC ta yabi Sadi Sani Sadiq
A wani labarin, kun ji cewa bidiyon caccakar Bola Tinubu da Sadiq Sani Sadiq ya yi ya dauki hankalin 'yan siyasa a Arewacin Najeriya.
Wani dan jam'iyyar adawa ta ADC, Ibrahim Garba Wala da aka fi sani da IG Wala ya fito ya yabawa jarumin, inda ya ce ya nuna kishin kasa.
An hango jarumin ya nuna yadda matsalolin tsaro suka karu a Arewacin Najeriya, musamman a Zamfara, Sokoto da sauransu a bidiyon da ya yi.
Asali: Legit.ng

