Kannywood Ta Girgiza: Fitaccen Mai Shirya Fina Finan Hausa, Nura Sharu Ya Rasu
- Masana'antar Kannywood ta shiga jimami sakamakon rasuwar babban furodusa Nura Sharif kuma na hannun daman Abdul Amart
- Abdul Amart Maikwashewa ya siffanta marigayin a matsayin mutumin kirki mai hakuri da dattako wanda ya rasu yana shirin tafiya Umra
- Hamisu Lamido Iyantama ya bayyana cewa marigayi Nura Sharu ya dade a masana'antar tun zamanin 'Linear' kafin zuwan kwamfuta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Masanaʼantar shirya fina finan Hausa ta Kannywood ta shiga jimami sakamakon rasuwar babban furodusa, Malam Nura Sharif.
Nura Sharu ya rasu ne a daren ranar Lahadi kuma an shirya jana'izarsa da karfhe 9:30 na safiyar Litinin 23 ga Fabrairun 2026 a gidan Sharif Hamidan da ke unguwar Dandago, Sabon Titin Mandawari a birnin Kano.

Source: Facebook
Furodusan Kanywood, Nura Sharu ya rasu
Babban furodusa, Abdul Amart Maikwashewa ne ya sanar da rasuwar Nura Sharu a shafinsa na Facebook, in da ya nuna matukar kaduwarsa da rashin abokin aikin nasa.
Abdul Amart Maikwashewa ya bayyana cewa:
"Na yi rashin masoyi… na yi rashin aboki… na yi rashin mutum na gari.
"Nura mutum ne mai haƙuri da ni, mai karɓar kuskure na cikin natsuwa, ba tare da ya nuna gajiya ko ƙorafi ba. Mutum ne mai dattako, mai nutsuwa, mai kyakkyawar zuciya. Duk wanda ya san shi ya san irin tarbiyyarsa da kyautatawarsa ga kowa.
"Wallahi ban san da wane kalami zan kwatanta shi ba. Halinsa ya wuce misali, dabi’unsa sun fi a iya fassara su da kalmomi. Allah Kaɗai Ya san raɗaɗin da nake ji a zuciyata yayin rubuta waɗannan kalamai. Rubutu ya gagare ni, hawaye suka fi kalmomi bayyana abin da ke raina.
"Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya yafe masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya ba mu haƙurin jure wannan rashi, Ya sa mu haɗu da shi a aljanna."
Sharu: 'Yan Kannywood sun yi jimami
Shi ma babban furodusa da ya ga jiya ya ga yau a Kannywood Malam Hamisu Lamido Iyantama ya bayyana Nura a matsayin gogaggen mai tace fim tun zamanin 'Linear' kafin zuwan kwamfuta, sannan daga baya ya zama mai sharyawa da bada umarni.
Ya ce sun yi aiki tare tsawon shekaru, har ma shi ne aka mika wa mukullan kamfanin Iyantama Multimedia a 1996 don kula da dukkan ayyuka a matsayin manaja, in ji rahoton Arewa Update.
Shi ma furodusa General BMB ya roƙi Allah ya gafarta wa Nura Sharif, ya wanke shi daga kura-kurai kamar yadda ake wanke farin kaya daga datti.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, General BMB ya ce:
"Allahumma ka gafarta wa Nura Sharif, ka jiƙansa da rahamar ka, ka wanke shi daga dukkan kura-kurai kamar yadda ake wanke farin kaya daga datti.
"Ka maye masa gurbin duniya da Aljannar Firdausi, ka haskaka masa kabarinsa, ka yalwata masa shi, ka haɗa shi da Annabi Muhammadu (SAW), Sahabbai da salihan bayi.
"Ya Allah, ka ba iyalansa, ‘yan uwansa da duk masoyansa hakuri da juriyar wannan babban rashi, ka ɗora su kan imani da yarda da ƙaddarar ka."

Source: Facebook
Karin ta'aziyyar rasuwar Nura Sharu
A nasa ɓangaren jarumi Muhammad T. Finisher da aka fi sani da Babawo a shirin Wata Shida ya ce mutuwar Nura ta zo masa a bazata, yana mai jaddada cewa mutuwa ba ta da sallama.
Shi ma babban amininsa Malam Sarari Lawal Muhammad na kamfanin Sarari Classic ya ce ya yi rashin amini, mutumin kirki wanda ya dauke shi a matsayin dan uwa duk da bambancin shekaru, inda ya roƙi Allah ya gafarta masa.
Furodusa Ali Rabi’u Ali ya bayyana Nura a matsayin mutumin kirki mai kiyaye dokokin Allah, ba shi da girman kai.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ali Rabi'u Ali ya ce:
"Kwanan nan muka kammala aikin SADDIQA na kamfanin Abnur-Entertainment da shi cikin mutunta juna. Har muka gama ya na cikin walwala saboda Abdul Amart ya biya masa Umra ya na shirin tafiya da azumi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya tausaya wa ma'aikata, ya masu wata garaɓasa a wurin aiki saboda Ramadan
"Komai aka yi masa ba ya fushi saboda ya na shaukin zuwa ganin babban masoyi Annabi Muhammad (SAW). Kwatsam ciwo ya tasam masa a watan azumi. Allah ya karbi ransa ya na mai niyya."
An rahoto cewa marigayi Nura Sharif shi ne ke jagorantar ɗaukar bidiyin tafsirin Sheikh Nasidi Abubakar Goron Dutse.
Mutuwar jaruman Kannywood kafin 2026
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsofaffin jarumai waɗanda suka kasance ginshiƙai tun lokacin kafuwar Kannywood, da kuma wasu matasan 'yan wasa sun rasu a 2025.
Da yawa daga cikin wadannan jarumai sun rasu ne a yayin da suke tsaka da taka rawa a wasu fina-fina, lamarin da ya sa aka maye gurbinsu da wasu.
Daga cikin jaruman Kannywood da suka rasu a 2025 akwai Maijidda Muhammad, wadda aka fi sani da Fulani a shirin fim mai dogon zango na Labarina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


