Bidiyo: Jaruma Samha Inuwa da Kotu Ta Ɗaure Wata 6 Ta Samu Kyautar ban Mamaki

Bidiyo: Jaruma Samha Inuwa da Kotu Ta Ɗaure Wata 6 Ta Samu Kyautar ban Mamaki

  • Fitacciyar jarumar Kannywood mai suna Samha M. Inuwa ta samu kyautar dalleliyar mota daga masoyinta da take wa laƙabi da 'Baby'
  • Hakan ya biyo bayan kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan gyaran hali bayan kama ta da laifin wulaƙanta Naira
  • Kyautar da Samha ta samu ya jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya bayan ta wallafa bidiyon motar ta miliyoyin Naira a shafinta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitacciyar jarumar Kannywood, Sa'adatu Muhammad Inuwa, wacce aka fi sani da Samha ta samu kyautar dalleliyar mota ƙirar Toyota.

Samha, wacce ta dade tana jawo ce-ce-ku-ce a intanet, ta samu kyautar motar ne awanni kaɗan bayan kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari.

Jaruma Samha M Inuwa ta samu kyautar mota bayan kotu ta yanke mata hukuncin daurin wata 6
Jarumar Kannywood, Samha M Inuwa kusa da sabuwar motar da 'Baby' ya bata. Hoto: @Samha_m_inuwa
Source: Instagram

Kotu ta daure jaruma Samha Inuwa

A bidiyon da jarumar ta wallafa a shafinta na TikTok, an ganta riƙe da jan ƙyalle fuskarta cike da walwala yayin da ta bayyana sabuwar motar da masoyinta wanda ta ke ma laƙabi da baby ya bata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano talakawan da suka fi bukatar taimako a Najeriya

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa wata babbar kotun tarayya da ke Kano, ta yanke wa jarumar hukuncin ne bayan hukumar EFCC ta shigar da ita kara.

Hukumar EFCC ta yi karar jaruma Samha ne biyo bayan bullar wani bidiyonta da ya nuna tana share majina da takardar Naira 'yan N1000, N1000.

Bayan ta amsa laifinta, Mai Shari’a S.M Shuaibu ya yanke wa Samha hukuncin daurin wata shida, ko kuma ta biya tarar N200,000.

An ba Samha kyautar sabuwar mota

Bayan an yanke mata hukuncin, rahoto ya nuna cewar jarumar ta biya tarar N200,000 da aka yanke mata, wanda yasa aka sallame ta nan take.

'Yan awanni kadan bayan sallamarta, sai kuma aka ga jarumar ta wallafa bidiyon sabuwar motar da 'baby' ya bata, wanda ake tunanin na dannar kirjin kamun da aka yi mata ne.

Binciken da Legit Hausa ta yi, ya nuna cewa farashin motar da aka sayawa jarumar, kirar Toyota Urban Cruiser a Najeriya ya bambanta dangane da shekarar da aka kera ta da kuma yanayin yadda take.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 200 sun shiga garuruwa 3 da Asubah, sun kashe mutane sama da 30

An fahimci cewa, farashin motar Toyata Urban Cruiser yana kai wa N45,000,000 zuwa N55,000,000 ko ma fiye da hakan.

Jaruma Samha M Inuwa ta samu kyautar dalleliyar mota daga 'Baby'
Jarumar Kannywood, Samha M Inuwa rike da makullin sabuwar motar da aka bata kyauta. Hoto: @samha_m_inuwa
Source: Instagram

Martanin jama'a kan bidiyon Samha

Kyautar danƙareriyar motar da 'Baby' ya ba Samha ta jawo ce-ce-ku-ce a kafar sada zumuntar zaman inda mutane ke tsokaci daban-daban.

A zantawar Legit Hausa da Yahanasu Khalid Zaria, ta yi mamakin yadda mutane ke fadin bakaken kalamai don jarumar ta samu irin wannan babbar kyauta.

"Ba tun yau ne muke kallon Samha tana cewa 'Baby' ya saya mata mota, ko ya bude mata shago ba. Mun sha jin sunan 'Baby' a bakin Samha, kenan bai kamata ya dada mutane da kasa ba.
"Yarinyar tana sharafi a yanzu, don haka, ko 'Baby' ko wasu mashinshinanta, za su yi rububin kyautata mata. Amma ranar da sharafin ya kare kuma fa? Kowa zai watse ya barta.
"Don haka, komai lokaci ne, a barta ta shana yanzu, lokacinta ne. Wata rana fa sai labari. Mun ga irinsu Murja Kunya, yanzu wa ke labarinta? Sai an yi dakyar ma ake tuna ta.

Kara karanta wannan

Ana ruguza allunan tallata Tinubu a Zamfara, ran jam'iyyar APC ya baci

"Akwai jarumai da suka yi tashi a shekarun baya, yanzu ba a ta su. Kuma ita duniya idan tana yinka, to za ta sanya maka girman kai ne, ba za ka ji wa'azin kowa ba, kawai fantamawa za ka sanya a gaba. Allah shi kyauta."

Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin mutane kamar haka:

@Amatullah:

"Idan ba arota akayi a gurin sarkin mota ba in sume."

@Zainab_dan_iya:

"Babbar damuwar ita ce, wa ya rubuta wa Samha taken rubutun nan?."

@abdulmalikyahayagwanki:

"Fatan alkairi hajjaju tabarakalLahu masha Allah."

@real_adamz_bwala:

"Ina taya ki murna, Allah ya sanya alheri hajiya."

@mustapha.alawi:

"Wai ni Samha ya maganar azumin gidan yarin ne, ko sai kin gama murnar sabuwar motar?"

Kalli bidiyon sabuwar motar Samha a nan kasa:

EFCC ta cafke jaruma Samha

Tun da fari, mun ruwaito cewa, EFCC ta cafke jarumar Kannywood Samha Inuwa a Jihar Kano bisa zargin goge majina da takardun Naira a cikin bidiyo.

'Yar wasar kwaikwayon tana tsare a ofishin hukumar yayin da ake gudanar da bincike kafin a gurfanar da ita a gaban kotun tarayya nan kusa.

Wannan kamu na nuna kudurin EFCC na kare darajar kudin kasar Najeriya da kuma hukunta duk wanda aka samu yana wulakanta Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com