An bawa Hadiza Gabon kyautar dankareriyar mota, hoto
Fitacciyar jaruma masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hadiza Gabon, ta yi murnar samun kyautar motar alfarma daga wurin wata kawar ta, Laila Ali Usman, shugabar kamfanin L and N interiors.
Jarumar ce da kanta ta sanar da labarin samun kyautar motar a shafinta na sada zumunta, wato Instagram tare da mik godiya ga aminiyar ta, Laila.
Hadiza Gabon ta rubuta "ina godiya Madam kudi, sabuwar mota ta @landinteriors ina godiya," cikin harshen turanci.
Tuni abokan sana'ar ta da na arziki ke cigaba da tururuwar turo sakon taya murna ga jaruma Hadiza Gabon.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng