Wata Sabuwa: Ana Zargin Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya Ya Bar Addinim Musulunci

Wata Sabuwa: Ana Zargin Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya Ya Bar Addinim Musulunci

  • An fara zargin jarumin Nollywood, Jamiu Azeez ya bar addinin musulunci bayan ganinsa ya halarci ibadar coci ta daren sabuwar shekara
  • Bidiyoyi da hotunan jarumin sanye da kayan coci sun haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin ya sauya addini
  • Jarumi Azeez ya maida zazzafan martani ga masu sukarsa, yana mai cewa mutane ba su da hurumin tsoma baki a kan sha'anin rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Mutane sun yi ca kan fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Jamiu Azeez bisa zarginsa da canza addini a sabuwar shekara.

Jarumin, wanda aka san shi a matsayin Musulmi ya haifar da ce-ce-ku-ce da rudani ne bayan an gan shi ya halarci ibadar coci ta daren sabuwar shekara.

Jamiu Azeez.
Jarumin fina-finan Nollywood, Jamiu Azeez Hoto: Jamiu Azeez
Source: Instagram

An fara zargin Jarumi Azeez ya canza addini

Kara karanta wannan

Kano: Wasu yara sun fadi dalilin murna da rasuwar mahaifinsu bayan shekaru 20

The Cable ta ruwaito cewa jarumin fina-finan Yarbawa, wanda aka fi saninsa da taka rawa a fina-finan iyali, ya fuskanci suka a kafafen sada zumunta bayan hotuna da bidiyoyinsa a coci sun bayyana a intanet.

Wasu na ganin hakan alama ce da ke nuna jarumin ya bar addinin musulunci, ya koma addinin kiristanci.

A cikin wani martani mai zafi da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, jarumin mai shekaru 40 ya yi watsi da wadannan zarge-zarge da kuma sukar da mutane ke masa.

Jamiu Azeez ya maida martani

Jarumi Jamiu Azeez ya kuma soki masu kokarin tsoma baki a cikin rayuwarsa ta sirri ba tare da dalili ba.

Azeez ya jaddada cewa zabin addininsa lamari ne na kansa, kuma ba dole ba ne ya nemi yardar kowa.

Jarumin ya kara da cewa bai dace mutane su rika yanke masa hukunci kan zabin rayuwarsa ba, yana mai cewa yana da ‘yancin bin duk addinin da ya ga dama.

“Ni dai a Najeriya ne kawai nake ganin mutane suna damuwa da rayuwar wani. Ku yi tunani da hankalinku, taya za ku gaya wa mutum mai shekaru 40 yadda zai rayu?

Kara karanta wannan

'Mutane sun fara guduwa,' Halin da ake ciki a Neja bayan kashe fiye da mutum 40

"Na wallafa hotona ina sanye da fararen kaya a wurin ibadar coci ta daren sabuwar shekara. Wasu ma sun biyo ni suna zagina. Babu wanda zai dauki alhakin rayuwata, ina da 'yancin zabar duk addinin da nake so, kuma hakan bai kamata ya damu kowa ba.
“Ban taba fitowa na ce na sauya addini ba. Kuna so ku kashe ni ne? Kada ku damu, gobe ma zan sa kayan Babalawo.”

- In ji Jarumi Jamiu Azeez.

Jamiu Azeez.
Fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood, Jamiu Azeez Hoto: Jamiu Azeez1
Source: Instagram

Auren jarumar Nollywood ya mutu

A wani labarin, kun ji cewa fitacciyar jarumar Nollywood, Anita Joseph, ta bayyana cewa aurenta da Fisayo Michael da aka fi sani da MC Fish Michael ya zo ƙarshe.

Jarumar ta kara da cewa ba ta da cikakkun amsoshi da mutane za su yi mata kan mutuwar auren, kuma ta yanke shawarar rungumar hakuri, juriya da imani da kaddarar Allah.

Tsawon watanni kafin wannan bayani, an dade ana rade-radin cewa auren Anita Joseph da MC Fish ya samu matsala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262