Malam Nata'ala da Wasu Fitattun Jaruman Kannywood da Suka Rasu a 2025

Malam Nata'ala da Wasu Fitattun Jaruman Kannywood da Suka Rasu a 2025

Yayin da masana'antar Kannywood ke ƙoƙarin farfaɗowa domin dawo da martabarta ta baya, musamman ganin yadda a bana aka fitar da ƙayatattun fina-finai masu inganci, a ɗaya ɓangaren kuma, masana'antar ta yi rashin wasu manyan jarumai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kamar yadda masu iya magana ke cewa "ana bikin duniya, ana na ƙiyama," hakan ya faru a masana'antar inda wasu jaruman suka rasu suna tsaka da taka rawa a wasu ayyuka, lamarin da ya sa aka maye gurbinsu da wasu.

Jaruman Kannywood da suka rasu a 2025
Maijidda Muhammad (Fulani) da Malam Nata'ala da suka rasu a 2025. Hoto: Labarina Series, Arewa24
Source: Facebook

Masana'antar ta rasa fitattun tsofaffin jarumai waɗanda suka kasance ginshiƙai tun lokacin kafuwar Kannywood, da kuma wasu matasan jarumai, in ji rahoton BBC Hausa.

Wannan ya sa bayan mun duba nasarorin da aka samu, muka ga dacewar waiwayar jaruman da suka riga mu gidan gaskiya a wannan shekara ta 2025 domin karrama gudunmawar da suka bayar.

Kara karanta wannan

An kama kasurgumin 'dan bindiga mai nuna miliyoyin kudi a intanet

1. Maijidda Muhammad (Fulani)

An yi jana’izar marigayiya Maijidda Muhammad, wadda aka fi sani da Fulani a shirin Labarina.
Jaruma Maijidda Muhammad ta rasu a ranar Alhamis, 25 ga Disambar 2025. Hoto: Labarina Series
Source: Facebook

An yi jana’izar marigayiya Maijidda Muhammad, wadda aka fi sani da Fulani a shirin fim mai dogon zango na Labarina, a garinta na Kontagora da ke jihar Neja, bayan rasuwarta a ranar Alhamis, 25 ga Disambar 2025.

Fulani ta rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya jefa masoya fina-finan Hausa, abokan aikinta da ‘yan uwa cikin tsananin alhini.

An wallafa a shafin Labarina na Facebook, cewa:

"Allah Ya yi wa ɗaya daga cikin jaruman shirin Labarina Series wato Jidda Muhammad Kontagora wadda aka sani da Fulani, matar Sarkin Gabas rasuwa.
"Hauwa'u Maijidda, wadda ta dade ta na fama da ciwon gyambon ciki, ta sha fama da jinya a baya-bayan wadda ta shafe kusan watanni biyu ta na kwance, kamin komawa ga Mahaliccin ta a Asibiti a yammacin wannan rana ta Alhamis, 25 ga watan Disambar 2025.
"Tabbas an yi babban rashi a kamfanin Saira Movies, la'akari da kasancewar ta ɗaya daga cikin manyan masu taka rawa a shirin Labarina Babi na Uku da mu ke tsaka da haskawa a yanzu haka."

Kara karanta wannan

Sojojin Amurka sun kawo hari Najeriya don 'kare rayukan kiristoci '

Tun da sassafe, jama’a daga wurare daban-daban suka rika tururuwa zuwa Kontagora domin yi mata bankwana na ƙarshe.

Manyan malamai ne suka jagoranci sallar jana’iza, inda aka yi addu’o’i na musamman domin Allah Ya gafarta mata, Ya kuma saka ta cikin Aljannar Firdausi. Daga nan aka raka gawarta zuwa makabarta inda aka yi mata sutura bisa koyarwar addinin Musulunci.

Abokan aikinta a masana’antar Kannywood, musamman na shirin Labarina, sun bayyana marigayiyar a matsayin mutumiyar kirki, mai ladabi da jajircewa, wadda ta bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa fina-finan Hausa.

2. Baba Karkuzu (Abdullahi Shuaibu)

Baba Karkuzu, jarumin Kannywood ya rasu ne a watan Maris, 2025.
Baba Karkuzu, jarumin Kannywood da ya rasu ne a watan Maris, 2025. Hoto: Zinariya
Source: Facebook

Fitaccen jarumin Kannywood mazaunin Jos, Abdullahi Shuaibu, wanda aka fi sani da Karkuzu, ya rasu, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

Jaridar ta rahoto cewa Karkuzu ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jos (JUTH) a ranar Talata, 25 ga watan Maris, 2025.

An gudanar da sallar jana'izarsa a safiyar ranar Laraba, inda ɗaruruwan masoya suka halarta. Ɗansa, Dalhatu Abdullahi, ya bayyana rasuwar mahaifinsa a matsayin babban rashi ga iyalansu. Karkuzu ya rasu yana ɗan shekara 94, ya bar mata ɗaya da yara shida.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi gaba da gaba da masu garkuwa da mutane a ranar Kirsimeti

Abokin aikinsa a masana'antar, Sani Mu’azu, ya ce:

“Abin da ya fi burge ni game da Karkuzu shi ne jajircewarsa da sadaukarwa ga aikinsa. Duk da ƙalubalen rayuwa da ya fuskanta, har da na rashin lafiya, ya ci gaba da fitowa a fina-finai har zuwa tsufansa, yana ƙarfafa matasan jarumai.
"Na san Karkuzu sama da shekaru 40, kuma zan iya shaida cewa haziki ne na musamman wanda ya bar gurbi a masana'antar fina-finai ta Najeriya.”

3. Malam Nata'ala (Mato Yakubu)

Allah ya yi wa Malam Nata'ala, jarumin Kannywood rasuwa.
Malam Nata'ala, jarumin Kannywood ya rasu ne a watan Nuwamba 2025. Hoto: Mahaluki Nata'ala Potiskum
Source: Facebook

A ranar Lahadi, 2 ga watan Nuwamba, 2025 ne Allah ya yi wa Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata'ala Mai Sittin Goma, rasuwa, a cewar rahoton Legit Hausa.

Malam Nata’ala, ɗan asalin Potiskum a jihar Yobe, ya yi suna ne sakamakon rawar da ya taka a matsayin malamin almajirai a shahararren shirin nan na Arewa24 mai suna ‘Daɗin Kowa’.

Marigayin ya fito a fina-finai da dama kafin ya shahara a shirin 'Daɗin Kowa'. An san shi da salon barkwanci, musamman wajen nuna malamin tsangaya mai yawan surutu amma abin dariya yayin da yake fama da matsalolin gida tsakanin mata biyu.

Kara karanta wannan

Gwamna Aliyu ya kaddamar da sababbin dabaru na kawo karshen ƴan bindiga a Sokoto

Rashin lafiyarsa ta jawo hankalin jama'a, har ta kai ga tara masa kuɗi, inda gwamnatin jihar Yobe da na Jamhuriyar Nijar suka shigo ciki don taimaka masa.

4. Umar Maikuɗi (Cashman)

Umar Maikuɗi ya rasu a watan Mayun 2025.
Umar Maikuɗi, jarumin Kannywood da ya rasu a Mayun 2025. Hoto: Labarina Series
Source: Facebook

A watan Mayun wannan shekarar ta 2025 ne jarumi Umar Maikudi (Cashman) ya rasu a Zaria da ke jihar Kaduna.

Legit Hausa ta rahoto cewa marigayin ya fito a shirin 'Labarina' mai dogon zango, sannan ya kasance shugaban ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Najeriya (MOPPAN) na ƙasa.

Hukumar amintattu ta MOPPAN da kuma babban taron fina-finai na ƙasa da ƙasa na Kaduna (KADIFF) ne suka sanar da rasuwar shugaban nasu.

Maikuɗi ya rasu a Zaria bayan ya daɗe yana fama da rashin lafiya kamar yadda rahoton jaridar Premium Times ya nuna.

Marigayin, wanda malamin koyar da harkar fina-finai ne kuma furodusa, an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar a farkon wannan shekarar, inda ya sa gaba wajen gina ƙwarewar mambobi da haɗin gwiwa domin bunƙasa masana'antar fina-finai ta Arewacin Najeriya.

5. Baba Hasin (Muhammad Shuaibu)

A ranar Asabar, 27 ga watan Afrilun wannan shekarar, ne kuma fitaccen jarumin nan Muhammad Shuaibu, wanda aka fi sani da Baba Hasin, ya rasu.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya samu mukami da shugaban jam'iyyar APC ya nada hadimai 15

Jarumin ya rasu ne yana ɗan shekara 68 a duniya bayan ya share tsawon lokaci yana jinya a Asibitin Malam Aminu Kano, kamar yadda aka samu rahoto.

Baba Hasin ya bar mata biyu da yara goma sha bakwai. An fi saninsa da halin girma da mutunci, ba ma a cikin fim ba kaɗai, har ma a rayuwarsa ta zahiri.

Daɗewar sa a cikin masana'antar ta sa ya kasance ɗaya daga cikin fuskokin da aka saba gani waɗanda suka taimaka wajen gina da kuma shaharar Kannywood a cikin shekaru da dama.

Tahir Fagge ya fadi halin da yake ciki

A wani labari, mun ruwaito cewa, fitaccen jarumin Kannywood, Tahir Muhammad Fagge, ya bayyana yadda ake kallon yan wasan Hausa da kuma kalubalensu.

Tahir Fagge ya koka kan rashin fahimtar jama’a da kuma yadda ake watsa bayanai marasa tushe game da sana'arsu, tare da jaddada cewa fim sana’a ce mai daraja.

Fitaccen jarumin, wanda a yanzu haka yake fama da ciwon zuciya, ya ce yana bukatar N2.5m domin jinyar sa a asibitin Abuja wanda Ali Nuhu ya taimaka masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com