CAN Ta Taso Jarumar Wasan Kwaikwayo a gaba kan Fim Din Kirsimeti, Matashiyar Ta Yi Martani
- Hukumar ta ce fina-finai ta bukaci fitacciyar jaruma ta sauya taken fim dinta da ya shirya mai alaka da Kirsimeti
- Fim din da jaruma, Ini Edo ta fitar ya tayar da kura wanda ake ganin ya yi karan-tsaye ga addinin Kiristanci
- Hakan ya biyo bayan korafi daga kungiyar Kiristoci ta Najeriya watau CAN inda ta soki jarumar game da fim din
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta dura kan jarumar wasan kwaikwayo bayan sakin shirinta da ke da alaka da Kirsimeti.
Hukumar Kula da Tace Fina-finai ta Kasa, NFVCB, ta bukaci jaruma kuma mai shirya wasa, Ini Edo, ta gyara taken fim dinta 'A Very Dirty Christmas'.

Source: Twitter
Idi Edo: Abin da Hukumar tace fina-finai ta ce
Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bayan koke daga Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, da wasu ’yan kasa dangane da sunan fim din, cewar Punch.
A cikin sanarwar da Shugaban Hukumar, Shaibu Husseini ya fitar, NFVCB ta ce tana mutunta bambancin addini da al’adu a Najeriya.
Hukumar ta bayyana cewa an amince da fim din ne bayan cikakken bincike da tantancewa daga Kwamitin Tace Fina-finai bisa labari da jigon sa.
NFVCB ta jaddada cewa amincewar taken fim din ba wai don raina Kiristanci ko Kirsimeti ba ne, illa a matsayin kirkirar labari.
Sai dai hukumar ta ce ra’ayin jama’a yana da muhimmanci, don haka ta bukaci furodusan fim din da ta sauya taken domin kauce wa tashin hankali.
Korafin kungiyar CAN game da fim din
Kungiyar CAN ta soki taken fim din tun da farko, inda Shugabanta, Rabaran Daniel Okoh, ya bayyana shi a matsayin abin takaici ga Kiristoci.
Okoh ya ce Kirsimeti lokaci ne mai tsarki da ke nuna haihuwar Annabi Isa Almasihu, wanda ke wakiltar tsarki, zaman lafiya da fansa.
Ya kara da cewa danganta kalmar “dirty” da Kirsimeti na rage darajar bikin, tare da mayar da shi abin wasa.

Source: Facebook
Martanin jaruma Edo kan fim dinta
A martaninta, Ini Edo ta ce ba ta da niyyar raina Kiristanci, tana mai jaddada cewa ita ma Kirista ce mai tsananin bin addini.
Ta bayyana cewa taken fim din na nuni da ma’ana ta alama, yana nuna sabanin da ke tsakanin farin ciki da kalubalen rayuwa.
Jarumar ta ce an dade ana tallata fim din a bainar jama’a ba tare da wani korafi ba, abin da ya ba ta mamaki yanzu.
Ini Edo ta gayyaci ’yan Najeriya su je gidajen sinima su kalli fim din, su fahimci sakon sa kafin yanke hukunci, cewar rahoton TheCable.
An fitar da fim din a ranar 16 ga Disamba, karkashin jagorancin darakta Akay Mason, tare da fitattun jarumai da dama.
Jarumar fim ta zargi maza da cin amana
A baya, kun ji cewa jaruma Bimbo Akintola ta caccaki mazan Najeriya, tana mai cewa kashi 99 cikin 100 duk su na cin manar matansu.
Fitacciyar jarumar ta ce al'adu kamar na auren mata fiye da daya na taimaka wa wajen cin amanar da maza ke yi a yanzu.
Ta bukaci yan uwanta mata su fuskanci gaskiya a zahiri, su daina rabuwa da samari ko mazansu saboda sun ci amanarsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


