Jarumin Kannywood Ya Fadi Halin Jinya da Yake Ciki, Ya Yaba Gudunmawar Ali Nuhu

Jarumin Kannywood Ya Fadi Halin Jinya da Yake Ciki, Ya Yaba Gudunmawar Ali Nuhu

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Tahir Muhammad Fagge, ya bayyana yadda ake kallon yan wasan Hausa da kuma kalubalensu
  • Ya koka kan rashin fahimtar jama’a da kuma yadda ake watsa bayanai marasa tushe, tare da jaddada cewa fim sana’a ce mai daraja
  • Fagge, wanda ke fama da ciwon zuciya, ya ce yana bukatar N2.5m domin jinyar sa a asibitin Abuja wanda Ali Nuhu ya taimaka masa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jarumin Kannywood, Tahir Muhammad Fagge ya bayyana kalubalen da yan wasan Hausa ke fuskanta a rayuwa.

Fitaccen jarumin wanda ya yi shura a harkar ya shawarci al'umma su rika yi musu kyakkyawan zato kan sana'arsu.

Jarumin Kannywood ya yabawa Ali Nuhu
Yan wasan Kannywood, Tahir Fagge da Ali Nuhu. Hoto: Kannywood Celebrities, Ali Nuhu Mohammed.
Source: Facebook

Tahir Fagge ya fadi dalilin rawa a gidan Gala

Fagge ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da jaridar RFI Hausa da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Omoyele Sowore ya bankado game da gwamnonin Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar da aka yi da shi a faifan bidiyo, Fagge ya koka kan yadda ake yi musu kallo inda ya ce fim sana'ace.

Ya ce ya hadu da rashin lafiya na ciwon zuciya, wanda yana neman taimako a wannan lokacin bai samu ba, yana gida yara suka zo suka ce sun bude wuri ya zama babban bako.

Ya ce:

"Ban je da zummar na yi wasa ba, na je da nufin ni babban bako ne a bude wurin na yi dawowa ta, ina neman N250,000 sun ba ni N100,000.
"Da na je an gama abin da za a yi, sai wani daga cikin yan kallo ya saka N100,000 cewa a dawo da wata tsohuwar waka yaran zamani su hau.
"Da suka yi ba daidai ba, sai aka ce ni na hau na dauki N100,000 na nuna musu yadda ake yi, amma kawai wani na jin haushinka sai ya yada ba tare da yin bincike ba."

Kara karanta wannan

Fitaccen jarumin fim a Najeriya ya saki bidiyo ana tsaka da jita jitar cewa ya mutu

Fagge ya ce duk wanda ya shawara a fim ana gayyatarsa gidan Gala inda ya kira manyan jaruman fim a Indiya da suke zuwa.

"Karkari a ce ai ba addininmu daya ba, fim ba addini ba ne, Hausa ba addini ba ce, yare ne amma ka fahimci addininka shi ne mafi muhimmanci."

- Tahir Fagge

Jarumi ya yabawa Ali Nuhu kan taimaka masa
Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu. Hoto: Ali Nuhu Mohammed.
Source: Facebook

Jarumi ya kwarara yabo ga Ali Nuhu

Tahir Fagge ya yabawa Ali Nuhu kan irin taimakonsa da yake yi yayin da yake fama da jinya a asibiti.

Ya kara da cewa:

"A yanzu haka jinya na ke yi karfin hali ne kawai, idan na kwanta wa zai ba ni, ina da iyalai, ko yanzu ina neman N2.5m a asibitin Abuja.
"Nan na ke zuwa a bincika, Ali Nuhu ne ya kai ni asibiti, muna fim din Alaka ya ce a tsayar da fim din ya dauka zazzabi ne ya ce a dakatar da fim din.
"Tun kafin mu karasa asiniti ya tura N1.5m duk wata shi yake sayamin maganin N150,000 har zuwa N180,000 duk kudin da kake samu a fim a wurin za aka cinye shi."

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sha alwashin hana Tinubu samun tazarce a 2027? Gaskiya ta fito

Nata'ala ya samu tallafi daga gwamna Buni

Kun ji cewa an yi ta sukar gwamnatin jihar Yobe game da rashin lafiyar dan wasan Kannywood, Mato Yakubu wanda aka fi sani da Malam Nata'ala.

Daga bisani gwamnatin Yobe ta yi duba kan lamarin jarumin inda ta shirya taimaka masa saboda halin da ya shiga na jinya mai tsanani.

Kwamishinan lafiya, Dakta Muhammad Lawan Gana, ya ce gwamnati za ta haɗa kai da asibitin domin tabbatar da ba shi kulawa ta musamman.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.