Nata’ala Ya Godewa Shugaban Nijar bayan ba Shi Makudan Kudi, Ya Taba Mala Buni
- Jarumin Kannywood Mato Yakubu, da aka fi sani da Nata’ala, ya bayyana farin ciki bayan samun tallafin kudin jinya daga Nijar
- Malam Nata'ala ya ce Shugaban kasa Janar Abdourahamane Tchiani ya tura masa miliyoyin kudi, ya yi godiya na musamman
- 'Dan wasan kwaikwayon ya na shan fama da jinya na cutar daji wanda ya bukaci taimako a baya saboda tuni karfinsa ya kare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Jarumin Kannywood, Mato Yakubu ya sake fitar da sabon bidiyo game da jinyar da yake fama da ita.
'Dan wasan da aka fi sani da Malam Nata'ala ya bayyana jin dadi bayan taimakon kudi da gwamnatin Nijar ta ba shi.

Source: Facebook
Makudan kudi da shugaban Nijar ya ba Nata'ala
Malam Nata'ala ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Nata'ala ya bayyana cewa Tchiani ya ba shi kyautar makudan kudi da suka kai CFA miliyan 10 (N27m).
Ya yi godiya na musamman inda ya ke kokawa kan yadda na kusa da shi suka bar shi amma bare suka taimaka masa.
Ya ce:
"Idan ka ga bidiyo na a baya duk na rame, yau 2 ga watan Satumbar 2025, shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya sa aka kira ni a waya, ya ce ina maka addu'a Allah ya tashi kafadunka, ya ce in tura asusun banki na.
"Wallahi kudin da shugaban kasar Nijar ya tura mani, ina tsoro ka da a yi mani aika-aika saboda kudin suna da yawa."

Source: Facebook
Nata'ala ya soki gwamnatin jihar Yobe
Malam Nata'ala ya ce gwamantin tarayya da jihar Yobe ba su taimaka masa ba, sun bar shi yana ta tangal-tangal da neman taimako.
Ya bayyana cewa tabbas wasu sun shiga tsakaninsa da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta fito da 'barnar' Malami a Kebbi, ta faɗi yadda tawagarsa ta riƙa harbin iska
Ya kara da cewa:
"Yau ga shi gwamnatin tarayya ba ta tallafa mani ba, gwamnatin jiha ta Yobe ba ta dauki nauyi na ba, ta bar ni ina tangal-tangal.
"A saka Tchiani a addu'a ina godiya sosai an ba ni kudi, jama'a ka da ku yi gaggawa nan da kwana kadan za ku ji yawan kudin.
"Ai idan mutum bai yi maka ba wani zai yi maka, kana ganin a gidana aka kini, jiha ta ta gagara daukar nauyi na.
"An shiga tsakani na da Mai Mala Buni, to sai ga kasar da ba tawa ba ta dauki nauyin jinyar.
Rashin lafiya: Nata'ala ya nemi taimakon al'umma
Mun ba ku labarin cewa jarumin Kannywood, Mato Yakubu wanda aka fi sani da Malam Nata’ala ya bayyana mawuyacin hali da yake ciki.
Malam Nata’ala mai turakar yasin ya tabbatar da cewa yana fama da cutar daji, inda ya bayyana bukatar taimakon addu’o’in al'umma da kudi.
'Dan wasan kwaikwayon ya godewa masu taimaka masa ciki har da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malaman addini da masana’antar Kannywood.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
