A Ƙarshe, Rahama Sadau Ta Fitar da Saƙo ga Masoya bayan Ɗaura Aurenta a Masallaci

A Ƙarshe, Rahama Sadau Ta Fitar da Saƙo ga Masoya bayan Ɗaura Aurenta a Masallaci

  • Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta tabbatar da cewa an ɗaura aurenta yau Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025 a jihar Kaduna
  • Rahama ta yi godiya ga Allah tare da nuna tsantsar farin cikinta da ta samu damar ganin wannan rana mai matuƙar muhimmanci a rayuwarta
  • Ta roki masoya da abokan arziki su sanya ta tare da angonta a addu'a, Allah Ya sa albarka a wannan aure kuma Ya ba su zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta tabbatar da labarin da ke ta yawo cewa an ɗaura aurenta yau Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025.

Jaruma Rahama Sadau ya bayyana farin cikinta da Allah ya nuna mata wannan rana da ta zama matar aure bayan bin duka matakan da adddinin Musulunci ya shar'anta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Abin da Amarya Rahama Sadau ta yi bayan ɗaura aurenta ya ja hankali

Jarumar Kannywood, Rahama Sadau.
Jaruma Rahama Sadau ta tabbatar wa masoya cewa ta yi aure Hoto: Rahama Sadau
Source: Instagram

Rahama ta yiwa ƴan uwa da al'umma godiya a wani sako da ta wallafa a shafinta na manhajar X tare da faifan bidiyo bayan ɗaura aurenta a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka ɗaura auren Rahama Sadau

Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa an ɗaura auren Rahama Sadau a wani masallaci a unguwar Rimi da ke Kaduna, ta auri wani bawan Allah mai suna Ibrahim Garba.

Ɗan uwanta, Abba Sadau ya shaidawa DCL Hausa cewa duka batun auren an yi shi ne a sirrance har sai ranar ɗaura aure sannan mutane suka sani.

A cewarsa, wannan aure da 'yaruwarsa ta yi yana ɗaya daga cikin burikan mahaifinsu, Malam Ibrahim Sadau, wanda Allah ya yiwa rasuwa sama da wata ɗaya da ya gabata.

Rahama Sadau ta aika saƙo ga masoyanta

A sakon da ta aike wa masoyanta bayan ɗaura auren, Rahama Sadau ta roki a sanya ta a addu'a Allah ya dawwamar da soyayya a gidanta kuma Ya sa wa auren albarka.

Kara karanta wannan

Wasiyyar da mahaifinsu Rahama Sadau ya bari kan auren ƴaƴansa kafin ya rasu

Rahama Sadau ta ce:

"Bismillahir Rahmanir Raheem, Alhamdulillah, an ɗaura min aure yau, na zama matar aure a hukumance, na shiga sabon babi a rayuwata. Zuciyata cike take da godiya da farin ciki.
"Ina rokon Allah Maɗaukaki Sarki Ya albarkaci wannan aure na mu da kwanciyar hankali, soyayya madawwamiya, farin ciki, da yalwar arziki.
"Muna roƙon addu’arku masoya yayin da (ni da ango na) muka shiga wannan sabuwar rayuwa ta ibada."
Jaruma Rahama Sadau ta yi aure.
Masoya sun yi wa Rahama Sadau fatan alheri bayan ta yi aure Hoto: Rahama Sadau
Source: Instagram

Yadda masoya suka yiwa amarya fatan alheri

Tuni dai masoya suka fara tururuwa sharhi a ƙasan sakon Rahama Sadau, inda galibi suke taya ta murna da kuma addu'ar Allah Ya ba da zaman lafiya.

Umar SPD ya ce:

"Ubangiji Allah Ya sa albarka, ina taya ki farin ciki, Allah Ya sa albarka, Amin."

Farida Idris ta ce:

"Masha Allah, Allah Ya sa wa aurenku albarka."

Bashir El-Bashir ya ce:

"Allah Ya maku albarka ke da mijinki, Ya haɗa ku a alkairi."

Wasiyyar da mahaifin Rahama Sadau ya bari

Kara karanta wannan

Biki bidiri: An daura wa jaruma Rahama Sadau aure a jihar Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa Haruna Ibrahim wanda aka fi sani da Abba Sadau ya tabbatar da daura auren a yau Asabar 9 ga watan Agustan 2025.

Abba ya bayyana cewa wasiyyar mahaifinsu da rasu ta karshe ita ce auren yayansa mata, wanda kuma yanzu sun fara cika masa.

Ya ce mijin Rahama mai suna Ibrahim ba dan Kannywood ba ne kuma ba a sako hotonsa ba saboda iyalansu sun ɓoye labarin auren ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262