"Ban Yafe ba," Jarumar Kannywood Ta Girgiza Intanet a Watan Ramadan, An Mata Martani

"Ban Yafe ba," Jarumar Kannywood Ta Girgiza Intanet a Watan Ramadan, An Mata Martani

  • Hadiza Aliyu Gabon ta bayyana cewa duk wanda ya zage ta ko ya ɗauki alhakinta ba ta yafe ba duk da an shigo watan azumi
  • Kalaman fitacciyar jarumar fim a masana'antar Kannywood sun ja hankalin mabiyanta, wasu na ganin hakan bai dace ba
  • Jarumar ta Kannywood ta ce duk wanda ya zage ta tana fatan Allah masa daidai da abin da ya yi mata, ta ce ba za ta haƙura ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan hausa watau Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta girgiza intanet bayan sanar da ganin watan Ramadan.

Hadiza Gabon ta ja hankalin mabiyanta a kafafen sada zumunta da ta wallafa cewa ba za ta yafe wa duk wanda ya ɗauki alhakinta ba duk da watan azumi ya tsaya.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Hadiza Gabon.
Jaruma Hadiza Gabon ta ja hankalin mutane bayan shiga watan azumi Hoto: @HadizaGabon
Asali: Twitter

Hadiza Gabon wacce ta shahara a Kannywood ta wallafa a shafinta na Instagram cewa duk wanda ya ci zalinta ba ta yafe masa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kalamai na jarumar na zuwa ne bayan watan azumin Ramadan na bana ya kama biyo bayan ganin jinjirin wata a daren jiya Juma'a, 28 ga watan Fabrairu.

Mai alfarma Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da cewa an ga wata, don haka yau Asabar, 1 ga watan Maris, 2025 ta kama 1 ga Ramadan.

Jaruma Hadiza Gadon ta ja hankalin jama'a

Sai dai yayin da musulmai musamnan a Arewacin Najeriya ke tura wa juna sakonni suna neman yafiyar juna kafin fara azumi, Hadiza Gabon ta ce ba ta yafe ba.

A sakon da ta wallafa, jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta bayyana cewa:

"Babu maganar wai an shiga watan azumi; duk abin da ka min ko kace a kai na, Allah Ya bi min haƙƙina.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba da belin Farfesa Usman Yusuf, ta gindaya masa sharuda

"Duk wanda ya san ya zage ni ban masa komai ba, Allah ya yi masa daidai abin da ya yi mani."
Hadiza Gabon.
Hadiza Gabon ta ce ba ta yafe wa duk wanda ya zage ta ba Hoto: Hadiza Gabon
Asali: Instagram

Mutane sun maida martani ga Gabon

Wannan dai ya jawo hankalin da yawa daga mabiyanta, inda wasu suka goyi bayanta a kan ka da ta yafe wa kowa, wasu kuma na ganin hakan bai dace ba.

Mahmoud Kitchen ta ce:

"Ashe dama ba ki son Allah ya yafe maki naki laifuffukan, ba mu sani ba ko ki na da yaƙinin ba ki laifin komai a wurin Allah.
"Manzon Allah SAW ya ce mafifici a cikinku shi ne wanda ya yi haƙuri, kuma haƙuri mafi kyau shi ne yafe abin da aka maka mara daɗi ko muzguna maka, Allah ya yi alƙawarin zai saka ma mai haƙuri."

Shehun Tiktok ya ce:

"Allah Ya isa dai kawai a taƙaice."

Adamsy Celebrity ya ce, "Kina kan daidai hajjaju."

Jarumar Kannywood ta kai mjinta ƙara

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum zai koya wa talakawa neman na kai a jihar Borno

A wani labarin kun ji cewa Jaruma Maryam Malika ta kai ƙara kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, ta nemi mijinta ya sawwaƙe mata.

Lauyan Maryam ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya yi furucin saki na uku shekaru biyar da suka wuce bayan ta nemi sakin ta, don haka zamansu ya ƙare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262