Hukumar Tace Finafinai ta Dakatar da Jarumar Kannywood, an Fadi Dalili

Hukumar Tace Finafinai ta Dakatar da Jarumar Kannywood, an Fadi Dalili

  • Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da jarumar Kannywood Samha M Inuwa na tsawon shekara ɗaya
  • Hukumar ta dakatar da Jarumar saboda yaɗa hotuna da bidiyoyin da suka ci karo da addinin da al'adun mutanen Kano
  • Hukumar ta sha alwashin ci gaba da tsabtace masana'antar ta Kannywood daga duk wasu abubuwan da ba su dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da fitacciyar jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, na tsawon shekara ɗaya, bisa zarge-zargen da ake yi ma ta na sanya tufafin da ba su dace ba, gami da yaɗa bidiyoyin da ke tayar da hankali.

Hukuncin ya bayyana ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaranta hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, biyo bayan korafe-korafe da dama daga jama’a kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ba kunya": Gwamna a Arewa da magabacinsa sun ɓarke da rawa a gaban sarki, bidiyo ya fito

Hukumar tace finafinai ta dakatar da jaruma Samha M Inuwa na shekara daya
Hukumar Tace Finafinai ta dakatar da jarumar Kannywood Samha M Inuwa saboda yada badala. Hoto: Samha_m_inuwa
Asali: Instagram

An sha gargaɗin Samha M Inuwa a baya

A cewar sanarwar, an sha gargaɗin jarumar game da sanya tufafin da ba su dace ba, da kuma yin kalamai na rashin tarbiyya a wasu daga cikin bidiyoyinta amma sai ta yi kunnen uwar shegu da duka gargaɗin da aka yi ma ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani mataki na ladabtarwa da hukumar tace finafinan ta ɗauka, ta sanar da cewa daga yanzu ta dakatar da tantance duk wani fim da jaruma Samha ta kasance ta fito a ciki.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan dakatarwar wani ɓangare ne na kokarin da hukumar ke yi na kiyaye kyawawan halaye a masana'antar shirya finafinan ta Kannywood da kuma tabbatar da bin ƙa'idojinta.

Hukumar za ta tabbatar da tsabtar masana'antar Kannywood

Hukumar ta jaddada cewa doka ta ba ta damar tabbatar da cewa duk wasu ayyukan ƙirkire-ƙirkire da suka haɗa da finafinai da rubuce-rubuce, sun yi daidai da tsarin addini, al’adu, da ɗabi’un al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Tsoron bincike ya sa SSG yin murabus a Bauchi? An gano gaskiya

Ta kuma bayyana cewa mutane da dama sun sha yin ƙorafe-ƙorafe da dama kan yadda jaruma Samha ke shiga ta rashin ɗa'a da kuma yaɗa wasu maganganun da ba su da ce ba a shafukanta.

Rahama Sadau ta bayyana wanda ya shigar da ita fim

A wani labarin na daban da Legit ta wallafa a baya, fitacciyar jarumar fim ɗin Kannywood Rahama Sadau ta bayyana wa duniya wanda ya shigar da ita cikin masana'antar Kannywood.

Jarumar ta bayyana cewa jarumi Ali Nuhu ne ya shigo da ita cikin masana'antar ta Kannywood bayan ganin wasan rawar da ta gudanar a wani gidan rawa da ke Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng