Bidiyo: Rahama Sadau Ta Cire Kunya, Ta Yi Rawar Ban Mamaki Tare da Umar M Shareef

Bidiyo: Rahama Sadau Ta Cire Kunya, Ta Yi Rawar Ban Mamaki Tare da Umar M Shareef

  • Rahama Sadau da Umar M Shareef sun gudanar da wasa tare a jihar Kaduna domin taya jama'a murnar shiga sabuwar shekara
  • An gayyato mawakairin su Umar M Shareef da Adam A Zango domin nishadantar da mutane a daren 1 ga Janairun 2025
  • Bidiyon wasan Rahama Sadau da Umar M Shareef ya janyo martani masu dadi daga masoyansu a kafafen sada zumunta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Kamar yadda suka saba nishadantar da mutane a cikin finafinai, a wannan karon ma Umar M Shareef da Rahama Sadau sun ja hankalin 'yan Kaduna.

A daren 31 ga watan Disamba, Rahama Sadau da Umar M Shareef suka gudanar da wasa tare a filin Murtala Square da ke Kaduna domin murnar sabuwar shekara.

Mutane sun yi magana yayin da Umar M Shareef da Rahama Sadau suka yi wasa a Kaduna
Umar M Shareef da Rahama Sadau sun gudanar da wasa na ban mamaki a Kaduna. Hoto: umarmshareef
Asali: Instagram

An yi taron murnar sabuwar shekara

Kara karanta wannan

An shiga cikin alhini da Gwamna Bala ya yi babban rashi a rayuwarsa

A wani bidiyo da Umar M Shareef ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar 1 ga Janairun 2024, an ga yadda jaruman biyu suka kwashi rawa gaban mahalarta taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar kowanne lokacin kaarshen shekara, ana shirya wani gagarumin taro a filin wasanni na Murtala, inda ake gayyatar mawaka da jarumai domin nishadantar da mutane.

A shekarar 2024, an gayyaci mawakan Kannywood da dama ciki har da Umar M Shareef, Adam A. Zango, Larabeey, Umar MB, DJ AB da sauransu.

Mawaka da jarumai har ma da masu wasannin barkwanci sun nishadantar da mahalarta taron har zuwa lokacin da aka shiga sabuwar shekarar 2025.

M. Shareef da Rahama Sadau sun yi wasa

A lokacin da mawaki Umar M Shareef ya shiga filin wasa, ya zo ne tare da jaruma Rahama Sadau, wacce dama aka saba ganinsu tare a irin wadannan bukukuwa.

A lokacin da suka hau wajen wasan, sun taka rawa sosai yayin da suke bibiyar wasu wakoki da Umar din ya yi ciki har da Rariya, Rayuwa Ta da sauransu.

Kara karanta wannan

An kama 'yan fashi 189, masu garkuwa 39 da 'yan daba 1,987 a Kano

Umar M Shareef ya yi wa al'ummar Najeriya barka da shigowa sabuwar shekara, tare da addu'ar Allah ya sanya ta zamo mafi alkairi ga al'umma baki daya.

Mutane sun yi martani ga bidiyon Umar

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin masu bibiyar jarumin a soshiyal midiya game da bidiyon rawar Rahama Sadau da Umar Shareef:

Abdulrasheed A Ladan:

"Sarki wanan haduwar ya farantamin."

Jabir Dan Chanji:

"Sarkin mawakan soyayya na Hausa."

Musa Bala Mb:

"Mai gidana ai ka sadu da alkairai da yawa kana ma cikin shi, sai dai ka taya mu da addu'a mu ma."

Yusuf Abdullahi:

"Amin, wai oga babu album ne wannan karshan shekarar?"

Yusuf Abdulrazak Salisu:

"Allah ubangiji ya kara basira Umar M Shareef."

Sadeeq Ibraheem:

"Allah Ubangiji ya kara basira da daukaka."

M Nasara Musa"

"Allah ya sa ka yi kyakyawan karshe Umar M Shareef."

Kalli bidiyon a kasa:

Jaruman Kannywood da suka fi yawan mabiya

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da 'yan Najeriya za su so ganin karshensu a 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla jarumai 10 na masana'antar Kannywood ne suka fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta a 2024.

Binciken da Legit Hausa ta gudanar ya nuna cewa Ali Nuhu ne dan wasan Kannywood mafi yawan mabiya a soshiyal midiya da mutane miliyan 8.5.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.