Kano Ta Cika Ta Batse: An Daura Auren Diyar Babbar jarumar Kannywood, Asma'u Sani
- Jihar Kano ta shaida taron manyan jarumai mata na masana'antar Kannywood a bikin Aisha, diyar jaruma Asma'u Sani
- Daushe Mai Dabaibayi, Abba El-Mustapha, Baballe Hayatu, Kawu Dan Sarki da sauransu na daga mazan da suka halarci bikin
- Tsofaffin jarumai, irinsu Mansura Isa, sun halarci bikin, tare da daukar hotuna masu kayatarwa a ranar kauyawa da kamu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Jihar Kano ta cika ta batse da manya manyan jaruman masana'antar Kannywood, inda suka halarci bikin diyar jaruma Asma'u Sani.
A yau Juma'a, aka daura auren Aisha, 'yar jaruma Asma'u Sani, daurin auren da ya samu halartar su Abba El-Mustapha, Baballe Hayatu da sauransu.
Jarumai sun halarci daurin auren Aisha
Mai shirya fina finan Hausa, Hamza Lawan Abubakar Dandago, ya wallafa bidiyon jarumai maza a wajen daurin auren a shafinsa na Instagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, an ga jarumin barkwanci, Daushe Mai Dabaibayi, Abba El-Mustapha, Baballe Hayatu, suna wasa da dariya da 'ya'yan Asma'u Sani a gabanta.
Kafin ranar daura aure, Hamza Dandago ya shaida cewa an gudanar da bukukuwa da suka hada da ranar kauyawa, ranar kamu, cin abincin dare da sauransu.
Mai Dawayya, Kawu Dan Sarki sun halarta
Har ila yau, mai shirya fina finan, ya wallafa wasu hotuna da bidiyo a shafinsa na Instagram, yana mai cewa:
"Kawu Dan Sarki da Aminu Mai Dawayya sun halarci kamu da ranar kauyawa na bikin 'yar gidan jaruma Asmau Sani a garin Kano. Muna fatan Allah ya sanya alheri."
A cikin hotuna da bidiyon da ya wallafa, an ga kusan dukkanin jarumai mata musamman wadanda suke fitowa a matsayin iyaye.
Wannan biki ya samu halartar tsofaffin jarumai irinsu Mansura Isa ta wallafa hotunanta tare da na sauran 'yan matan Kannywood da suka dauka a wajen bikin.
Mawaki Auta Waziri ya zama ango
A wani labarin, mun ruwaito cewa an daura auren fitaccen mawakin Kannywood Auta Waziri a ranar 6 ga watan Disambar 2024 a jihar Kaduna.
Mawakin ya wallafa wasu zafafan hotunan kafin aurensa tare da sahibarsa Halima Mustapha, ya gayyaci 'yan uwa da abokan arziki zuwa bikin nasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng