'Ku Biya Haraji': Fitaccen Mawakin Arewa Ya Saki Bidiyon da Ya Jawo Masa Zagi
- Fitaccen mawakin Arewa, DJ AB, ya gamu da suka mai zafi bayan ya saki bidiyon da ya bukaci 'yan Najeriya su biya haraji
- Mabiyan DJ AB sun nuna rashin jin dadin bidiyon da ya saki, suna ganin cewa bai dace ya yi wannan maganar yanzu ba
- DJ AB ya kare kansa, yana mai cewa biyan haraji wajibi ne, amma mabiyansa sun yi barazanar daina bibiyar wakokinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Mawakin Hip Hop na Arewa, Haruna Abdullahi (DJ AB) ya gamu da fushin 'yan soshiyal midiya bayan ya saki wani bidiyo kan biyan haraji.
DJ AB na shan suka saboda ya saki bidiyonsa a dai dai lokacin da ake ci gaba da adawa da kudurorin gyaran haraji na Shugaba Bola Tinubu.
Wane bidiyo ne ya jawowa DJ AB zagi?
A ranar 11 ga watan Disamba, DJ AB ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook, wanda ya yi wa taken: "Mu biya haraji domin gina Najeriyar da muke fata."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, mawakin ya yi maganganu da suka nuna muhimmancin biyan haraji da kuma amfanin da ake yi da kudaden harajin da aka tara.
Mawaki DJ AB ya bukaci 'yan Najeriya da su hada kai da hukumar tattara haraji ta kasa wajen biyan hakkokinsu na haraji domin samar da ababen more rayuwa.
'Yan Arewa sun yiwa DJ AB tatas
To sai dai da alama wannan bidiyo na DJ AB bai yiwa masu bibiyarsa dadi ba, inda mafi akasari suk nuna rashin jin dadinsu a kan maganganun da ya yi.
Mabiyan DJ AB wadanda da yawansu 'yan yankin Arewa ne, sun yi barazanar daina bibiyar wakokinsa yayin da wasu kuma ke ruwan tsinuwa a kansa.
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanononin jama'a kan bidiyon DJ AB.
Abdallah Hussain:
"Biyan haraji ba matsala ba ne amma me za mu amfana da shi bayan mun biya? Ya kamata ka bi a sannu ko ka rasa mabiyanka saboda ka yi maganar a lokacin da ba ta dace ba."
Mukhtar Umar
"Biyan haraji ba siyasa ba ne, hakki ne da ya rataya a kan duk dan kasa, ban ga laifin wannan bidiyon ba."
Mubarak Bashir
"Ba ka da lafiya. Shi ya sa sam ban wani damu da kai ba. Abin mamaki ne mutum kamarka ka fito kana wa'azi a kan biyan haraji bayan ka san halin da aka jefa kasar."
EL Yaqub Mohammed:
"AB ka janye jiki daga siyasa. Dole yanzu ka kare sana'arka. Ka ga wannan bidiyon da ka saki har ya sa na rage kaunar wakokinka."
OR SA MA:
"Gaskiya babban yaya ba ka da kishin Arewa wallahi kudai idan jifa ta tsallake ku ta fada kan kowaye."
Kalli bidiyon hade da sauran martanin jama'a a kasa:
Momee Gombe ta sa an kama Khadija
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitacciyar jarumar Kannywood, Momee Gombe ta sa 'yan sandan Kano sun cafke 'yar TikTok, Khadija Mai Bakin Kiss.
Momee Gombe ta bayyana cewa ta dauki matakin ne domin kare kanta daga zargin da Khadija ta yi mata na cewa tana yin madigo da kanwarta Meemah.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng