Fitaccen Mawakin Kannywood Zai Angwance Ranar Juma'a, An Saki Zafafan Hotuna
- Fitaccen mawakin Kannywood, Auta Waziri na gayyatar 'yan uwa da abokan arziki zuwa daurin aurensa a ranar 6 ga Disamba
- Wata sanarwa da Legit Hausa ta gani ta nuna cewa mawaki Auta Waziri zai angwance ne da sahibarsa Halima Mustapha
- Mawaki Auta Waziri, ya wallafa wasu zafafan hotunan kafin aure da ya dauka tare da kyakkyawar amaryar da zai aure
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Shahararren mawakin Kannywood, wanda tauraruwarsa ke haskawa a kasashen da ke jin wakokin Hausa, Auta Waziri zai angwance.
Auren da Auta Waziri zai yi ya zama abin magana a shafukan sada zumunta, musamman bayan bullar zafafan hotunansa tare da amaryar da zai aura.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Auta Waziri ya shaidawa abokan sana'arsa da ma masoyansa cewa 'lokacin da zan shiga daga ciki ya yi.'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a daura auren Auta Waziri
A cikin sanarwar, Auta Waziri ya ce:
"Ina farin cikin gayatar yan uwa da abokan arziki zuwa daurin aure na in sha Allah a ranar Jumma’a mai zuwa, 6 ga watan Disamba wanda za a daura a masallacin Jumma’a da ke SMC Unguwan Dosa a jihar Kaduna da misalin karfe daya na rana."
Wani gajeren bidiyo da mawakin ya wallafa hade da sanarwar ya nuna cewa Auta Waziri, wanda asalin sunansa Abdullahi Abubakar zai angwance ne da Halima Mustapha (Marmah).
Zafafan hotunan kafin Aure na Auta Waziri
Jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa ne kuma kafofin sada zumunta suka cika da zafafan hotunan kafin aure na mawaki Auta Waziri.
Mawakin da kansa, ya wallafa hotuna daban daban wanda ya dauka tare da kyakkyawar amaryarsa, lamarin da ya jawo fadin albarkacin bakin masoyansa.
Kalli hotunan kafin auren a kasa:
Mawaki El-Muaz Birniwa ya kwanta dama
A wani labarin, mun ruwaito cewa mawakin Kannywood, El-Muaz Muhammad Birniwa ya rigamu gidan gaskiya a daren ranar Alhamis, 4 ga watan Disamba.
An rahoto cewa El-Muaz ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ya ke buga kwallon sada zumunta da aka shirya na bikin mawaki Auta Waziri a jihar Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng