An Shiga Jimami a Kannywood Yayin da Jaruma Rahama Sadau Ta Yi babban Rashi
- Jarumar fina finan Hausa, Rahama Sadau, ta sanar da rasuwar kakarta wadda ta ce ta taka rawa daga yarinta zuwa girmasu
- A ranar Alhamis, ta wallafa a shafukan sada zumunta cewa mutuwa ta ziyarce su, kuma sun rasa wani bangare na rayuwarsu
- Tuni dai jarumai, abokan sana'a da kuma masoyan Rahama Sadau suka rika tururuwar taya ta alhinin wannan babban rashi da ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta yi babban rashi yayin da kakarta ta rigamu gidan gaskiya.
Jaruma Rahama Sadau ta nuna tsananin kaduwarta da rasuwar kakar ta ta, wadda ta ce ta nuna masu gata da soyayya a lokacin da take raye.
Kakar Rahama Sadau ta rasu
A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar 28 ga Nuwamba, Rahama Sadau ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A yau mutuwa ta ziyarce mu kuma mun rasa wani bangare na rayuwarmu. Kakarmu wadda ta taka rawa a rayuwarmu ta rigamu gidan gaskiya.
"Muna rokon Allah ya jikanta da Rahama, ya sanya ta a gidan Aljannah Firdausi."
Jarumar ta kara da cewa:
"Allah ya jikanki Hajiya. Allah ya yi miki rahama, ya sa Aljannah ce makoma a gareki. Ameen.
"InnalilLahi wa inna iLaihir rajiun."
Kalli sanarwar a nan kasa:
'Yan Kannywood sun shiga alhini
falalu_a_dorayi:
"Allah ya jikanta ya ba ku hakurin rashinta."
salisufulani10
"Allah ya gafarta mata Ameen."
salisufulani10
"Allah ya mata rahama. Muna ta'aziyya."
real_maryamyahaya
"Allah ya mata rahama."
official_hairat11
"Allah ya gafarta mata, ya yi mata rahama."
madam__korede
"Allah ya sa ta huta."
officialmaryambooth
"Allah ya mata rahama."
nafeesat_official
"Allah ya yi mata rahama."
Tinubu ya ba Rahama Sadau mukami
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rahama Sadau ta samu mukamin mamba a kwamitin shirin saka hannun jari a fannin kirkire-kirkiren zamani (iDICE).
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya kaddamar da shirin domin tallafawa masana'antar kirkire-kirkire ya sanar da mambobin kwamitin.
A yayin kaddamar da shirin, Shettima ya ce majalisar zartarwar Najeriya ta amince a fitar da $617.7m domin gudanar da shirin a jihohi 36 na kasar ciki har da Abuja.
Asali: Legit.ng