'Yan Kannywood Sun Fusata da Ganin Bidiyon da Ake Lakadawa Dan Bilki Kwamanda Duka
- Mawaka da wasu daga cikin jaruman Kannywood sun nuna fushinsu kan wani bidiyo ya nuna ana lakadawa Dan Bilki Kwamanda duka
- Ga wadanda ba su sani ba, Kwamanda wani fitaccen 'sojan baka' ne wanda ya ke yawan sharhi kan lamuran siyasa musamman a Kano
- Mawaki kuma mai shirya fina-finai, Nazifi Asnanic ya bayyana abin da ya faru da Dan Bilki abin bakin ciki, la'akari da dimokuradiyya ake yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tun bayan da wani faifan bidiyo ya bulla a shafukan sada zumunta wanda ya ke nuna yadda aka lakadawa Dan Bilki Kwamanda duka, jama'a ke ta ce-ce-ku-ce.
Ga wadanda basu sani ba, Dan Bilki Kwamanda wani fitaccen 'sojan baka' ne wanda ya ke yawan sharhi kan lamuran siyasa musamman a Kano da jihohohin Arewa.
Bidiyon yadda ake dukan Dan Bilki Kwamanda
A wani bidiyo da Muhammad Adam Tudun Murtala ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga Dan Bilki Kwamanda cikin ankwa a hannu, ana yi masa tambayoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda ke yi masa tambayoyin suna tuhumar sojan bakan da "zagin gwamnan Kaduna, Uba Sani" tare da neman jin dalilin da ya sa yake tsoma baki a siyasar jihar.
A yayin da shi Dan Bilki Kwamanda ke kokarin kare kansa, an ga fusatattun wadanda ke masa tambayoyin suna tsula masa bulala, yayin da suke magana cikin fushi.
Kalli bidiyon a kasa:
Kannywood ta dauki fushi kan bidiyon
Bayan bullar wannan bidiyon, wasu daga cikin mawaka da jaruman Kannywood sun fito sun nuna fushinsu kan dukan da aka yi wa Dan Bilki Kwamanda.
Mawaki kuma mai shirya fina-finai, Nazifi Asnanic ya ce abin da aka yi wa Dan Bilki Kwamanda abin bakin ciki ne la'akari da cewa dimokuradiyya ake yi a Najeriya.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X hade da bidiyon, Asnanic ya ce:
"Dimokuradiyya a Najeriya, abin bakin ciki ne."
Darakta a masana'antar Kanywood, Sanusi Oscar 442 ya ce ya san duka ba zai taba hana Dan Bilki Kwamanda yin shiru da bakinsa ba.
"Na san shi ciki da bai dinsa, da kun yi hakuri da sharrinsa, to da ku na zaune za ku ga sakayya daga Allah."
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram, Usman Mu'azu, mai shirya fina-finai ya nuna adawa da dukan da aka yiwa Dan Bilki Kwamanda inda ya ce:
"Dokar kasa ta hana cin zarafin dan Adam, idan ya yi laifi, kotu ce take yanke hukunci ba dan sanda.
"Hakika ya kamata a bi masa hakkin sa."
An saba garkame Dan Bilki Kwamanda
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kotun majistare dake zamanta a Kano ta tasa keyar Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda zuwa gidan gyaran hali.
A lokacin an gurfanar da Dan Bilki Kwamanda a kotu ne kan zargin batanci da sharri wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng