Bayan Rahama Sadau, Wata Jarumar Fina Finai Ta Sake Samun Mukami a Abuja
- Kakakin Majalisar Wakilan tarayya, Tajudden Abbas ya naɗa jarumar fina-finan Nollywood mukami a ofishinsa
- Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya ba Eniola Badmus muƙamin hadimansa a bangaren harkokin al'umma da tsare-tsare
- Badmus tana daya daga cikin jarumai da suka ba da gudunmawa da goyon bayan jam'iyyar APC a zaben da ya wuce
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jarumar fina-finan Nollywood, Eniola Badmus ta samu muƙami daga kakakin Majalisar Wakilai, Tajudden Abbas.
Abbas ya naɗa Badmus Eniola a matsayin hadima ta musamman kan korafin al'umma da tsare-tsare da kuma bukukuwa.
Goyon baya da jarumar ta ba APC
Nadin jarumar ya bayyana ne a yau Juma'a 10 ga watan Mayu bayan yada shi a kafofin sadarwa, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumar ta yi kaurin suna wurin nuna goyon bayanta ga jam'iyyar APC duk da irin kushewa da caccakar da ta sha a wurin jama'a.
Sai dai wannan nadin na jarumar ya jawo kace-nace a tsakanin al'ummar Najeriya, PM News ta ruwaito.
Wasu jama'a da dama sun taya ta murnan samun wannan mukami yayin da wasu ke kushewa.
Martanin mutane kan nadin Badmus
@TaoFeek182:
"Wannan nadin ya dace da ke, na miki murna, kin dage wurin tabbatar da kasancewa cikin jam'iyyar kafin da kuma bayan zabe, bai kamata a manta da ke ba."
@Alpha_Femalee:
"Yanzu na gane meyasa ta dage a zaben da aka gudanar, na miki murna da samun hadima ga kakakin Majalisar Wakilai, Tajudden Abbas."
@BlummyZusi:
"Badmus ta samu abin da ta ke nema tuntuni, amma ai zasu gina mata ofis saboda ban gane irin wannan mukami ba."
Rahama Sadau ta samu muƙami
A wani labarin, an ji Gwamnatin Tarayya ta nada jarumar fina-finai Rahama Sadau a matsayin mamba a kwamitin gwamnati da ke kula da shirin saka hannun jari .
Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Ibrahim Shettima ne ya kaddamar da kwamitin a Abuja.
Shirin iDICE hadin guiwa ne tsakanin gwamnati da hukumomin duniya da suka hada da bankin masana'antu da bankin raya Afrika.
Asali: Legit.ng