'Yan Kannywood Za Su Dara Sosai a Gwamnatin Abba Gida Gida, In Ji Jarumi El-Mustapha

'Yan Kannywood Za Su Dara Sosai a Gwamnatin Abba Gida Gida, In Ji Jarumi El-Mustapha

  • Fitaccen jarumin fim ɗin Kannywood, Abba El-Mustapha ya ce 'yan fim za su dara a gwamnatin Abba Gida Gida
  • Abba ya ce gwamnatin Kwankwaso ta taimaki 'yan masana'antar ta Kannywood ta hanyar basu tallafi da dama
  • Ya kuma koka kan yadda gwamnatin da ta shuɗe ta Abdullahi Ganduje ta karya masana'antar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Fitaccen jaruminnan na masana'antar Kannywood, Abba Ruda, wanda aka fi sani da Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa yan wasan fina-finan Hausa za su dara a wannan gwamnati ta Abba Gida Gida.

Ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kanon Dabo.

Abba El-Mustapha ya ce gwamnatin Abba Gida Gida za ta duba 'yan fim
El-Mustapha ya ce 'yan Kannywood za su dara a gwamnatin Abba Gida Gida. Hoto: Abba El-Mustapha1
Asali: Facebook

Abba ya ce an taimaki 'yan fim a lokacin Kwankwaso

Abba El-Mustapha ya ce a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, an taimaki jaruman masana'antar ta Kannywood ta hanyoyi da dama.

Kara karanta wannan

"Ku Cire Tsoro" Gwamnan Arewa Ya Yi Karin Haske Kan Matakai 2 da Zai Ɗauka Kan Malamai 7,000 A Jiharsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga ciki a cewar El-Mustapha, har da fitar da wasu daga cikin 'yan masana'antar da aka riƙa yi zuwa ƙasar waje domin su ƙaro ilmi kan yadda za su gyara harkokinsu.

Ya kuma ƙara da cewa waccen gwamnatin ta Kwankwaso, ta riƙa bai wa 'yan Kannywood tallafi da rancen kuɗaɗe domin su bunƙasa harkokinsu.

Sai Abba ya koka kan cewa gwamnatin Ganduje da ta zo, ta yi watsi da wannan tsarin da ake yi a gwamnatin Kwankwaso.

Ya ƙara da cewa sai bi aka riƙa yi ana kama 'yan masana'antar ta Kannywood ana ɗaurewa, sannan kuma aka bi hanyoyi da dama wajen karya masu sana'ar.

An daƙile harkar fim a gwamnatin Ganduje

Abba El-Mustapha ya kuma bayyana cewa an ɗakile masu harkar fim da kuma mawaƙa masu hikima a lokacin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta shuɗe.

Kara karanta wannan

Daga Karshe El-Rufai Ya Bayyana Gaskiyar Ma'anar Kalaman Da Ya Yi Kan Hanyar Da Shugaba Tinubu Ya Ci Zabe

Sai dai El-Mustapha ya ba da tabbacin cewa gwamnatin Abba Gida Gida za ta duba masana'antar ta Kannywood domin yi ma ta abinda ya kamata.

A kalamansa:

“Ni dai na san tabbas cewa a wannan gwamnati mai albarka ta Injiniya Abba Kabir Yusuf, Abba Gida Gida ko ka ce Abba mai gyarau, tabbas ɗan fim zai dara zai yi dariya za kuma a ci gaba daga inda aka tsaya.”

Abba ya kuma bayyana cewa babban burinsa shi ne ya ga masana'antar ta Kannywood na gogayya da sauran masana'antun shirya finafinai na duniya.

Abba ya kuma shawarci abokan sana'arsa ta fim da su dage su ƙaro karatu musamman ɓangaren abinda ya shafi sana'arsu domin inganta ta.

Matashi ya nemi 'yan Kannywood su nema masa auren Zainab Indomie

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wani matashi Abdussamad Ishaq da ya bayyana cewa yana muradin auren fitacciyar jarumar nan Zainab Indomie.

Kara karanta wannan

Na Yi Wa Jam'iyyar APC Kamfe Amma Ta Bani Kunya, Fittaciyar Jarumar Fina-Finai Na Najeriya

Matashin ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Fesbuk, biyo bayan bayyana kalar mijin da jarumar ke so da ta yi yayin da aka yi hira da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng