Wani Matashi Ya Nemi Jaruman Kannywood Su Nema Masa Auren Jaruma Zainab Indomie

Wani Matashi Ya Nemi Jaruman Kannywood Su Nema Masa Auren Jaruma Zainab Indomie

  • Shahararriyar jarumar masana'antar finafinan Kannywood, Zainab Indomie ta sace zuciyar wani matashi wanda yake son yin wuff da ita
  • Matashin ya nuna aniyarsa ta auren jarumar inda ya tabbatar da cewa idan ta shirya to shi ma a shirye yake a sha biki
  • Matashin mai suna Abdussamad ya bayyana dalilan da ya sanya yake son ya yi wuff da jarumar ta masana'antar Kannywood

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi ya nuna aniyarsa ta auren shahararriyar jarumar masana'antar finafinan Kannywood, Zainab Indomie.

Matashin mai suna Abdussamad Ishaq ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Matashi na neman yin wuff da Zainab Indomie
Matashin ya ce a shirye yake idan jarumar ta shirya Hoto: Abdussamad Ishaq
Asali: Facebook

Matashin dai ya yi wannan rubutun ne bayan jarumar ta bayyana irin kalar mijin da ta ke so a wata hira da aka yi da ita a shirin Gabon's Room Talk Show.

Kara karanta wannan

"Ya Daina Nuna Mun Soyayya" Wata Mata Ta Roki Kotu Ta Raba Auren Kuma Ta Umarci Mijin Ya Riƙa Biyanta N30,000

A hirar jarumar ta bayyana cewa tana son samun miji wanda zai ji tausayinta, zai karɓe ta a yadda ta ke, mai tausayi, mai adalci, mai gaskiya, wanda zai ƙaunaceta ta ƙaunace shi wanda ba kuma zai sauya daga kan gaskiyarsa ba koda kuwa zai yi mata kishiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya shirya tsaf domin auren Zainab Indomie

Abdussamad ya bayyana cewa da gaske yake kuma da zuciya ɗaya akan maganar auren jarumar idan dai har ta shirya ba da wasa ta ke yi ba domin jan hankalin mutane.

A cewarsa a shekarun da yake da su a duniya jarumar ta cika sharuɗɗan irin macen da yake son aura a rayuwarsa.

A kalamansa:

"Allah ya ga zuciyata da niyyata. Indai ba wasa ta ke ba, ko ta faɗa domin jan hankalin mutane ba, to a cewa Zainab Indomie ta samu mai aurenta."

Kara karanta wannan

"Wahala": Magidanci Ya Garzaya Kotu Neman a Raba Aurensa Da Matarsa, Kotu Tace Ba Aure a Tsakaninsu, Ta Bayar Da Dalili

"A shekaru irin nawa ni fa macen da ta san rayuwa tafi daɗin sha’ani ba wacce ƙuruciya ke mata fitsari akai ba, shiyasa ta burgeni da tace “Namiji mai tausayi, mai hakuri wanda zai aureta a yadda take shi ta ke so, kuma bazata hanashi ƙara aure ba”. Wannan ma dalilai ne da zasu sanya na so Zainabu"
"Aure dai ƙaddara ne, kuma nayi imani da hakan, wannan dalilin ne ma yasa."
"Wallahi sai naji tausayinta ya kamani, sannan tsaf zan iya auren Zainabu Abu, idan har da gaske take ace mata na shirya wallahi."

Ya buƙaci manyan ƙusoshi a masana'antar ta Kannywood irinsu Tahir Ibrahim Tahir, Falalu A. Dorayi da Hadiza Aliyu Gabon su zama shaida akan wannan ƙudirin nasa. Ya ce zai yi hakan ne ba domin neman suna ba

Ya tabbatar da cewa idan har jarumar ta amince to shi ma ya amince inda ya yi addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi a ciki.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Ajiye Girman Kai, Ta Isa Gaban Saurayinta Da Zobe Domin Neman Aurensa, Hotuna Sun Yadu

Legit Hausa ta samu jin ta bakin Abdussamad Ishaq wanda ya tabbatar da cewa maganar da ya yi domin son auren Zainab Indomie, babu wasa a cikinta.

Matashin ya bayyana cewa ko kaɗan babu maganar wasa a cikin kalamansa. Inda ya nuna cewa da gaske yake son ya aureta.

Ya bayyana cewa yanzu jarumar ba ɗaukaka gareta ba ballantana ace saboda ita yake sonta ba, ba kuɗi gareta ba ballantana ace su ne suka ruɗe shi yake sonta.

"Hirar ta da na ji hankalina ya kwanta da ita, na ji hankali da hangen nesa a cikin zantuttukanta." A cewarsa.

Jaruman Kannywood Da Suka Taba Yin Soyayya Da Juna

A wani labarin kuma, mun tattaro mu ku jerin jaruman masana'antar Kannywood da suka taɓa yin soyayya da junansu a masana'antar ta finafinan Hausa.

Jerin ya fara ne tun daga soyayar jarumi Adam A. Zango da wasu manyan jarumai mata biyu na masana'antar, waɗanda soyayyar su har kusa aure ta kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng