Ali Madagwal Ya Fice Daga Tafiyar Kwankwasiyya Bayan Ya Kasa Samun Shiga

Ali Madagwal Ya Fice Daga Tafiyar Kwankwasiyya Bayan Ya Kasa Samun Shiga

  • Ali Madagwal ya fice daga tafiyar siyasar Kwankwasiyya ta gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Maɗagwal ya fice daga Kwankwasiyya ne bayan ya kasa samun shiga a wajen gwamnatin jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar
  • Fitaccen mai wasan barkwanci ya koma jam'iyyar APC wacce dama yake a cikinta kafin gudanar da zaɓen gwamnan jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Shahararren mai wasan barkwanci a masana'antar finafinan Kanywood, Ali Artwork wanda aka fi sani da Maɗagwal, ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa Maɗagwal ya fice daga tafiyar ta Kwankwasiyya ne bayan ya kasa samun fada a gwamnatin jam'iyyar NNPP da ke mulki a jihar Kano.

An fahimci Ali Maɗagwal ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ne bayan ya ɗora hotonsa tare da na ɗan takarar jam'iyyar APC na gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, a shafinsa na Facebook inda rubuta “Gawuna is coming. Kano First.”

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sabon Shugaban Yan Sandan Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan Bayan Gaje Baba

Ali Artwork ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya
Ali Madagwal tare da Nasiru Yusuf Gawuna Hoto: Madagwal
Asali: Facebook

A baya an san Ali Artwork a cikin tafiyar Kwankwasiyya inda yake goyon bayan gidan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, Madagwal ya sauya sheƙa a lokacin zaɓen 2023, inda ya sulale zuwa jam'iyyar APC domin goyon bayan ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, A.A. Zaura.

Bayan komawarsa APC, ya buɗe wa Kwankwaso aiki inda ya bayyana cewa tafiyar ta Kwankwasiyya bata tsinana masa komai ba.

Ya bayyana cewa ya gaji ba zai iya ci gaba da tafiyar da ko sisi ba a ba shi a tsawon shekara 10 da ya kwashe a cikin tafiyar.

Ya sake dawowa Kwankwasiyya bayan Abba ya ci zaɓe

Sai dai kwatsam jam'iyyar NNPP na yin nasara a zaɓen gwamnan jihar Kano, sai ya tattaro ƴan kayansa ya dawo tafiyar Kwankwasiyya inda ya koma yabon sabon gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Naɗa Kwamishinoni 19, Ya Tura Sunayensu Ga Majalisar Dokokin Kano

Sai dai, a wannan karon bai ji da daɗi ba domin duk wata hanyar da zai shiga Kwankwasiyyar da kyau an doɗeta. Hakan ya sanya ya tattara kayansa ya koma APC.

Yanzu dai ya ci gaba da tallan Gawuna da AA Zaura a shafukansa na sada zumunta.

Madagwal Ya Caccaki Abba Gida-Gida

A wani labarin kuma, kun ji yadda Ali Artwork wanda aka fi sani da Madagwal, ya yi suka kan rushe-rushen da gwamnan jihar Kano yake ta aiwatarwa a jihar.

Madagwal ya ce hakan kuskure domin ba shi ne haƙiƙanin abinda al'ummar jihar Kano su ke buƙata ba kenan a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel