Hotunan Wankan Cakarewar da Matan Kannywood Suka yi Wurin Shagalin ‘Margi Day’ a Biki Halima Atete

Hotunan Wankan Cakarewar da Matan Kannywood Suka yi Wurin Shagalin ‘Margi Day’ a Biki Halima Atete

  • Kyawawan matan masana’antar Kannywood sun matukar kawata wurin shagalin auren jaruma Halima Yusuf Atete wanda aka yi a Maiduguri dake Borno
  • Wankan da suka yi ya matukar daukar hankalin jama’a shi ne na Margi day wato ranar da aka bayyana al’adar jaruma Halima Atete
  • Daga cikin fitattun jaruman da suka dire Maiduguri akwai Hadiza Gabon, Samira Ahmad, Fati Yola, Sadiya Mohammed Gyale, Maryam Yahaya da sauransu

Maiduguri, Borno - Fitattun jaruman Kannywood mata sun cika kwan su da kwarkwatar su a wurin shagalin auren jaruma Halima Yusuf Atete wacce aka fi sani da Halima Atete.

Jaruman masu tarin yawa sun tattara komatsansu tare da direwa a garin Maiduguri wanda shi ne babban birnin jihar Borno inda suke yin kara ga jarumar kan auren da take yi.

Sanannu daga cikinsu akwai Samira Ahmad, Hadiza Gabon, Fati Yola, Sadiya Gyale, Maryam Yahaya, Momee Gombe da sauransu.

Kara karanta wannan

Mata Sun Cika Wajen Gangamin Bola Tinubu, Matar Shugaban Kasa ba ta Iya Zuwa ba

Babu shakka zuwansu ya matukar karawa wurin auren armashi ballantana cakarewar da matan suka yi da shigar kabilar Margi wanda shi ne yarensu Halima Atete.

Legit.ng Hausa ta kawo muku labarin cewa, jarumar zata amarce da kyakyawan Angonta Mohammed Mohammed Kala a garin Maiduguri dake Borno.

A yanayin tsarin shagalin auren jarumar, an buga wasan kwallon kafa a ranar Laraba, ranar Alhamis an yi shagalin ranar Margi, washegari aka biye bikin da daren Larabawa sannan aka daura aure a ranar Asabar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan daura auren ne aka garzaya inda aka yi shagalin liyafar cin abincin dare sannan aka mika amarya dakinta. Ga wasu daga cikin hotunan:

Jaruman sun matukar bayar da kala a wurin shagalin bikin na jaruma Halima Atete.

Hotunan kafin bikin jaruma Halima Atete sun kayatar

A wani labari na daban, kyawawan hotunan kafin aure na jaruma Halima Atete sun matukar birge jama’a yayin da suke shirin aure da masoyinta.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Jingine Siyasa, Ya Bayyana Mutumin Da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasa a 2023

A zuka-zukan hotunan da suka bayyana na kafin aure, an ga jarumar da angonta mai suna Mohammed Moha Kala wanda za a daura aurensu a ranar 26 ga watan Nuwamban 2022.

Tuni dai abokan sana’art, ‘yan uwa da abokan arziki suka fara tururuwarw taya kyakyawar jarumar murnar cigaban da take shirin samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng