Alkawari ya Kusa Cika: Za a Daura Auren Rukayya Dawayya da Afakallahu Ranar Juma’a

Alkawari ya Kusa Cika: Za a Daura Auren Rukayya Dawayya da Afakallahu Ranar Juma’a

  • Katin gayyatar daurin auren jaruma Rukayya Umar Santa tare da masoyinta Isma’il Na’Abba Afakallahu ya bayyana a kafafen sada zumuntar zamani
  • Kamar yadda katin dauren auren ya bayyana, za a daura auren a ranar Juma’a mai zuwa a Masallacin Juma’a na Timasha dake Kano da karfe 2
  • Angon ya sanar da cewa yana gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki amma ga wadanda basu samu damar zuwa ba su bi su da addu’a

Kano - Labari mai dadi da Legit.ng Hausa ke samo muku shi ne na fitar katin daurin auren Jaruma Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya da masoyinta Alhaji Isma’ila Na’Abba Afakallahu

Rukayya Dawayya
Alkawari ya Kusa Cika: Za a Daura Auren Rukayya Dawayya da Afakallahu Ranar Juma’a. Hoto daga @labarankannywood
Asali: Twitter

Kamar yadda shafin Labaran Kannywood na Twitter ya wallafa, za a daura auren masoyan a ranar Juma’a mai zuwa, 4 ga watan Oktoban 2022 da karfe biyu na rana.

Kara karanta wannan

Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan ‘Yan Boko Haram, Sun Aike Wasu Lahira

wallafar tace:

”Gayyatar daurin auren shugaban Hukumar Tace fin-finaI, Isma’il Na’abba Afakallah tare da tsohuwar jaruma Hajiya Rukayya Dawayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

”Wanda za a yi rabar Juma’a 4 ga watan Oktoban 2022 a Masallacin Juma’a na Timasha da misalin karfe 2:00 na rana.
”Allah yasa alkhairi.”

Ango Alhaji Isma’ila Na’Abba Afakallahu ya sanya katin a shafinsa na Instagram inda yake gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki tare da bukatar addu’a ga wadanda ba zasu samu damar halartar daurin auren ba.

“Alhamdulillah muna gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki, idan ba a samu dama ba a yi mana addu’.”

- Angona Hajiya Rukayya Dawayya ya rubuta yayin wallafa katin.

Jarumar ma wata amarya Rukayya Dawayya ba a bar ta a baya ba, ta sake wallafa katin da angonta ya wallafa a shafinta.

Ayiriri: Shirin Shagalin Auren Rukayya Dawayya da Afakallah Ya Kankama

Kara karanta wannan

‘Dan Sanda Ya Sokawa Abokin Aikinsa Almakashi Yayin da Suke Baiwa Hammata Iska

A wani labari na daban, Shekara na zuwa karshe aurarraki na cigaba da yawaita. Hankulan wasu ‘yan fim ya koma kan aure kuma ana ta jiran auren Hajiya Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya da shugaban Hukumar tace fim na Kano, Isma’il Na’am ba wanda aka fi sani da Afakallahu.

Mujallar fim ta samu zantawa da wasu a masana’antar Kannywood duk da sun bukaci a sakaya sunayensu kan tsumayen bikin da suke yi.

A batun auren, majiyar ta sanar da cewa:

“Ba yanzu aka fara batun auren ba. Ko makaho a Kannywood ya san akwai soyayya a tsakanin Afakallah da Dawayya.
“Abu ne da aka jima ana yi a kasan kasa ba tare da an bayyanawa duniya ta sani ba. A yanzu da aski yazo gaban goshi ne yasa Rukayya ta fara dora hoton Afakallah a status na WhatsApp, TikTok da Instagram tare da bayanai masu nuna alamun soyayya dake da karfin gaske.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel