A Karon Farko, Rahama Sadau Ta Bayyana Abinda Taji Bayan MOPPAN Ta Dakatar Da Ita

A Karon Farko, Rahama Sadau Ta Bayyana Abinda Taji Bayan MOPPAN Ta Dakatar Da Ita

  • Jaruma Rahama Sadau ta caccaki masana’antar Kannywood da Hukumar Tace Fina-finai ta MOPPAN kan dakatar da Safara’u
  • Sadau ta bayyana cewa, ko a ido aka kalla jaruma Safara’u za a iya gane cewa tana cikin matsananciyar damuwa wacce ta taba ta sosai
  • Fitacciyar jarumar da aka saba dakatarwa a Kannywood tace bata taba shiga damuwa ba don an dakatar da ita, illa iyaka tayi murmushi

Fitacciyar jarumar fim Rahama Sadau ta caccaki masana’antar Kannywood da Hukumar Tace fina-finaI kan yanda aka dakatar da Jaruma Safiya Yusuf wacce aka fin sani da Safara’u bayan bayyanar bidiyonta.

An dakatar da Safara’u daga masana’antar fina-finan Hausa a shekarar 2022 bayan bayyanar bidiyonta.

Rahama Sadau
A Karon Farko, Rahama Sadau Ta Bayyana Abinda Taji Bayan MOPPAN Ta Dakatar Da Ita. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Dukkan Yara 11 da ta Haifa Makafi ne Kuma Ita ke Kula Dasu a Bidiyo Mai Taba Zuciya

Zakakurar jarumar tace kawayenta ne suka fitar da wannan bidiyonta wanda hakan ya durkusar da sana’arta a wannan lokacin.

Safara’u ta fara shuhura ne a fim mai dogon zango wanda gidan talabijin din Arewa 24 suke haskawa mai suna Kwana Casa’in, tace ta yi zaman gida na tsawon watanni uku domin gujewa zagin jama’a.

Jarumar ta kara da cewa sai da ta kusa goge dukkan asusunta na soshiyal midiya saboda zagin da take sha daga jama’a. Sai dai iyayenta da ‘yan uwanta sun bukaci ta rungumi hakan matsayin kaddara.

Rahama Sadau tayi martani

Sai dai a ranar Litinin, Rahama Sadau ta caccaki MOPPAN da suka dakatar da Safara’u, Premium Times ta rahoto.

An dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood a karon farko a watan Maris din 2015.

“Ina jin cewa bai dace masu tace fina-finai da su dakatar da jarumar ba saboda bidiyonta ya bayyana. Yadda suka bi don shawo kan lamarin bai dace ba. Mutum ce kuma hakan zai iya saka ta a damuwa.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: NAF Sun Sheke Rikakken Shugaban ‘Yan Bindiga, Ali Dogo

“Idan ka kalla bidiyon tattaunawar ta da BBC zaka gane cewa bata ji dadin faruwar hakan ba kuma ta shiga damuwa.
“An dakatar dani daga Kannywood sau da yawa amma abin bai taba damuna ba. Duk lokacin da suka sanar da dakatarwan na kan kalla in yi murmushi.
“Safara’u na fama da matsalar kwakwalwa. Mutanen dake dakatarwa ko korar jama’a mutane ne da basu da fuskoki. Ban taba sanin wanda ya dakatar da ni ba a lokacin da aka dakatar da ni saboda basu da fuskoki.
“Tambaya ta garesu shine me yasa suke saurin dakatar da jama’a ko korarsu a kan kuskure kadan? Hakan bai dace ba.”

- Rahama Sadau tace.

Na Yafewa ‘Yan Ta’addan: Budurwar da Kwamandan Barayin Fasinjojin Jirgin Kasa Yaso Aure

A wani labari na daban, Lois Azurfa, budurwa mai shekaru 21 da kwamandan ‘yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya so aura, ta bayyana irin ukubar da ta sha yayin da take hannun ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

Arzurfa wacce ke cikin ragowar fasinjoji 23 da aka saki ranar Laraba da ta gabata ta sanar da manema labarai yayin da take gadon asibiti.

Ta kara da cewa ta yafewa ‘yan ta’addan da suka azabtar da su tun bayan da suka sace su a ranar 28 ga watan Maris a farmakin da suka kai wa jirgin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel