Abun Mamaki: Bidiyon Matar da ta Haifa Yara 11 dukkansu Makafi, da Yadda Take Kula dasu

Abun Mamaki: Bidiyon Matar da ta Haifa Yara 11 dukkansu Makafi, da Yadda Take Kula dasu

  • Cike da abun mamaki, wata mata ta haifa yara 11 wadanda dukkansu makafi ne tun daga haihuwarsu duk da likitoci sun sanar mata cewa lafiyarsu kalau
  • A wani bidiyo da aka saki a YouTube, matar wacce mijinta ya rasu tace tana gwagwarmaya ita kadai wurin kula da makafin ‘ya’yanta
  • Labarin ya firgita jama’a da yawa wadanda suke ta mamakin me zai sa matar ta haifa yara haka wadanda dukkansu babu ido

Bidiyon Agnes Nespondi, wata mata ‘yar kasar Kenya wacce ta haifa yara 11 duk makafi ya dauka hankali a YouTube.

Bidiyon mai tsayin mintuna 8 da sakan 10 an wallafa shi ne a a Afrimax na Turanci kuma ya bayyana mahaifiyar tana kokarin kula da yaranta.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun Kama Wiwi ta N4m wacce Za a Kai wa ‘Yan Ta’adda a Yobe

Born Blind
Abun Mamaki: Bidiyon Matar da ta Haifa Yara 11 dukkansu Makafi, da Yadda Take Kula dasu. Hoto daga YouTube/Afrimax
Asali: UGC

Agnes tace dukkan yaranta ta haifesu da makanta duk da likitoci sun fada mata cewa kowanne ciki da ta dauka lafiyayye ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dukkan ‘ya’yan sun girma banda biyun karshe da har yanzu yara ne. Sai dai har yanzu babu wani gamsasshen bayanin lafiya dake nuna dalilin makantarsu.

Ma’abota amfani da YouTube sun yi tsokaci

Lerato Linkie tace:

“Soyayyar dake tsakanin uwa da ‘da ta har abada ce.”

Everlyne Moraa tace:

“Ina fatan ubangiji ya kula da mahaifiyar. Ita gwarzuwa ce dake kula da dukkan yaranta duk da nakasarsu. Ki cigaba da aiki me kyau uwa tagari.”

Arenla Jamir yayi tsokaci da:

“Ubangiji ka albarkaci wannan mahaifiya da kyawawan ‘ya’yanta. Soyayya daga Indiya.”

Muriel Johnson yace:

“Bani da kalaman da zasu fallasa abinda ke zuciyata game da yaran nan. Zan aiko muku da tallafi.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Yar Najeriya ta mutu yayin da ake mata tiyatar cikon mazaunai a India

Alfred Lungu yace:

“Wani sai yayi tunanin yana muguwar rayuwa ne amma akwai wanda yafi shi wahala sosai. Allah kayi mana rangwame.”

Lucy Mwenje yace:

“A duk lokacin da na ganta, ina kallon buri ne.”

Anet Menjemela tace:

“Kai, wannan akwai abun mamaki. Shaidan ya kai mummunan farmaki ga wadannan iyali. Allah ya kawo mata sauki. Daga Zambia nake kallon wannan.

Bayan Shekaru 4 da Rasuwar Mahaifiyarta, Budurwa Ta Bayyana Bidiyo Mai Taba Zuciya na Yadda Rayuwa Ta Kasance

A wani labari na daban, bidiyon da wata budurwa ta fitar bayan rasuwar mahaifiyarta da shekaru hudu tana bayyana yadda rayuwa ta kasance cike da gwagwarmaya da fadi-tashi ya taba zukata.

Kamar yadda bidiyon ya yadu kuma arewafashion style suka saka a shafinsu na Facebook, budurwar ta labarta yadda rayuwarta da ta ‘yan uwanta ta kasance bayan mutuwar mahaifiyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel