Jaruma Rahama Sadau Ta Maida Zazzafan Martani Kan Sanya Sunanta a Kamfen Tinubu
- Rahama Sadau, jaruma a masana'antar Kannywood, ta nesanta kanta daga tawagar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu
- Da take martani bayan ganin sunanta ɓaro-ɓaro, Sadau tace bata da masaniyar yadda sunanta ya shiga tawagar matan
- A ranar bikin zagayowar samun yancin kan Najeriya, APC mai mulki ya ayyana tawagar kamfe ta mata
Shahararriyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta nesanta kanta daga jerin sunayen tawagar Kamfe, wanda ya ƙunshi fitattun mata da zasu yi aiki tukuru don a zaɓi Bola Tinubu na APC a zaɓen 2023.
A Daftarin mai ƙunshe da shafi 70, aƙalla an ga sunayen jaruman Kannywood da Nollywood 33, waɗanda suka samu shiga tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ta mata.
Yayin da take nesanta kanta daga jerin sunayen, Shahararriyar Jarumar yar arewacin Najeriya tace labarin, "Babbar ƙarya ce mara tushe."
Da take ƙaryata labarin a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita, Rahama Sadau ta rubuta cewa, "Wannan babbar ƙarya ce, ba ni da masaniya kan lamarin, ban san ta ya sunana ya shiga ba, ba ni da alaƙa ko ɗaya da batun."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar 1 ga watan Oktoba, 2022, watau ranar da Najeriya ta samu yancin kanta daga turawa, jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da jirgin mata na yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa.
Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, Sanata Oluremi Tinubu da Hajiya Nana, matar Sanata Kashim Shettima, su ne zasu jagoranci tawagar kamfe ta mata.
Daga cikin jaruman da suka shiga tawagar sun haɗa da Joke Silva a matsayin shugabar rukuni, Fausat Balogun, Remi Oshodi, Mercy Johnson, Rose Odika, da Sola Kosoko.
Lanre Hassan (Iya Awero) Hajiya Nas, Lizzy Jay (Omo Ibadan), Princess Kalihat Bello ɗa dai sauransu duk an ga sunayensu a cikin tawagar.
Tinubu ya naɗa Aisha Buhari jagorar tawagar kamfe na mata
A wani labarin kuma Tinubu Ya Nada Aisha Buhari Matsayin Jagorar Mata A Kamfensa, Ba Sunan Matar Osinbajo
Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta APC, ta sanar da nada Matar shugaban kasa Aisha Buhari a matsayin wadda zata jagoranci mata a kamfen din jami’iyyar na 2023, a yau asabar.
Kwamittin mai taken “Tawagar mata masu kamfen din Tinubu/Shattema” ana sa ran uwargidan shugaban kasa itace zata zama shugabar din wannan tawagar.
Asali: Legit.ng