Yadda Aka Yi Na Fara Soyayya Da Marigayiya Balaraba Har Ta Kaimu Ga Aure, Lawan Kumurci

Yadda Aka Yi Na Fara Soyayya Da Marigayiya Balaraba Har Ta Kaimu Ga Aure, Lawan Kumurci

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Shu'aibu Lawan Kumurci ya bayyana yadda soyayya ta kullu tsakaninsa da marigayiya Balaraba har ta kaisu ga aure
  • Kumurci ya ce mahaifin Balaraba ya sanar masa cewa a baya ko fim dinsa bata son kallo saboda yadda yake fitowa a dan daba
  • Sai dai kuma ya ce da Allah ya nufa matarsa ce sai ga shi sun kai ga aure amma basu da rabon zama tare a matsayin mata da miji a nan duniya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu’aibu Lawan Kumurci, ya magantu a kan soyayyarsa da marigayiyar matarsa, jaruma Balaraba.

A wata hira da ya yi da sashin BBC Hausa a shirin 'Daga bakin mai ita', Kumurci ya bayyana cewa sun fara haduwa ne da jarumar a wajen daukar wani shirin fim inda suka shigo suka tarar da ita a zaune.

Sai dai kuma, jarumin yace ya lura da yadda marigayiyar ta dunga kallonsa amma sai shi ya dauke kai daga wajenta don kada ta tsargu da yawan kallo.

Balaraba da Kumurci
Yadda Aka Yi Na Fara Soyayya Da Marigayiya Balaraba Har Ta Kaimu Ga Aure, Lawan Kumurci Hoto: Facebook/kannywood news/Instagram/real_kumurci
Asali: UGC

Da aka kammala daukar shirin sai ya sanar da abokan sanar’arsa inda suka ce hakan ba wani abu bane kasancewarsu jarumai, shima sai ya yarda da hakan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jarumi Kumurci ya ce washegari da suka sake dawowa sai ta nemi da suyi hoto tare da shi inda shi kuma yace a’a kasancewar abokinsa Sani Mai Iska ne ya kawota wajen kuma kada ya zo bai ji dadin abun ba.

Sai Marigayiya Balaraba tace masa babu komai dama saboda shine ta zo wajen, hakan yasa ya hakura suka yi hoton. Bayan nan ta neme shi ta kuma bashi hoton da ya fito.

Jarumin ya ci gaba da cewa ana haka ne Marigayiya Aisha Dan Kano ta same shi ta fada masa cewa Balaraba ta nuna tana sonshi amma sai yake ganin ba gaskiya bane domin a ganinsa a wancan lokacin, ta fi karfinsa.

Ya ce har ransa ya ji dadin wannan batu amma kuma sai yana ganin shi bai kai ta so shi ba sai sai idan tana da wani muradi a kansa, sai abokansa suka ja hankalinsa har dai ya yarda suka kulla soyayya.

Bayan ya je gidansu ne kuma sai ya gano ashe abun ya fara ne daga chan domin har mahaifinta ya bashi wani dan labari game da yadda abun ya fara.

Kumurci ya ce:

“Mahaifina ya ce wato in baka labari a da ita Balaraba mamana yake kiranta don yafi sonta a cikin yaransa, da duk sanda aka kawo fina-finai idan dai da naka ciki bata kallo za ta fara zagi shi wannan dan daba shikenan kashe mutane, shi cutar da mutane.
“Sai mahaifin nata yace kika san inda rana zata fadi, sai tace menen haka, sai aka fassara mata kika sani ko ki dawo kina sonsa ko ya aure ki. Sai tace Allah ya kiyaye wannan dan daban.

“Lokaci da fim din Ukuba ya fito sai yaje masu chan sai aka ce mata ai mutumin naki yayi fim mai kyau, sai tace masu ita ba zata kalla ba.
“Toh bayan sun gama gani ta je ta dawo sai ta dauka sai ta saka, da ta sa sai ta rufe kofa sai tana kalla, sai tana mayar da wurin da nayi aiki a kai tana kalla. Sai mahaifin nata da ya dawo ya gani sai ya kira yan uwan nata gaba daya yace toh ku zo ku gani, sai suka leko suna gani sai suka yi mata dariya sai kunya ta kamata.
“Toh shikenan dai wannan abun kamar wasa shine kuma Allah kawo yayi matata ce shine har muka zo aka yi aure sai kuma Allah yayi nufin ba za mu zauna anan ba, Allah ya ji kanta da rahma.”

Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya

A wani labarin kuma, jama’a sun shiga rudani bayan bayyanar wasu hotuna na manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ado Gwanja da Momee Gombe a soshiyal midiya.

A cikin hotunan wadanda tuni suka yadu a shafukan sadarwa, an gano jaruman biyu cikin shiga da ta fi kama da ta sabbin ma'aurata kuma sun yi tsayuwar daukar hoto sak irin na amarya da ango.

Wannan al’amari ya jefa mutane cikin shakku, yayin da wasu ke ganin shirin fim ne, wasu kuma sun yi fatan Allah yasa hakan ya zamo gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel