Kannywood: Mafi Yawancin Mutane Za Su Saka Jaruman Fim A Wuta Idan Aka Ba Su Dama, In Ji Hauwa Waraka

Kannywood: Mafi Yawancin Mutane Za Su Saka Jaruman Fim A Wuta Idan Aka Ba Su Dama, In Ji Hauwa Waraka

  • Fitacciyar Jarumar masa'antar fina-finan arewa, Kannywood, Hauwa Abubakar ta ce mafi yawancin mutane suna yi wa jarumai zato mara kyau
  • Jarumar da aka fi sani da Hauwa Waraka ta ce galibin mutane za su saka jaruman a wuta idan su ke da wuta da aljanna
  • Hauwan ta ce bata damu da irin kallon da mutane ke mata ba domin ta san ta yi imani da Allah da manzonsa kuma bata shaye-shaye ko karuwanci sai dai domin fadakarwa ne ta ke taka irin rawar a fim

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hauwa Abubakar, da aka fi sani da Hauwa Waraka a Kannywood, ta ce mutane da dama za su tsinduma jarumai a wuta idan suna da dama, Daily Trust ta rahoto.

Waraka, wacce ta bayyana hakan yayin hira da BBC a ranar Alhamis, ta nuna bacin rai kan zargi marasa kyau da mutane ke yi wa jarumai mata.

Kara karanta wannan

2023: Ku Dena Yin Sojan Gona Da Sunan Mu, CAN Ta Gargadi Yan Siyasan Najeriya

Hauwa Abubakar aka Hauwa Waraka.
Kannywood: Mafi Yawancin Mutane Za Su Kai Jarumai Wuta Idan Aka Ba Su Dama, In Ji Hauwa Waraka. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumai fina-finan wacce aka haifa a Jos kuma ta girma a Kano, ta fuskanci zargin rashin da'a a masan'antar.

Musulmi daga arewa sun sha sukar ta saboda tana fitowa a yanayi da ke nuna wasu halaye marasa kyau da musulunci ba ta amince da su ba kamar karuwanci da ta'amulli da miyagun kwayoyi.

Wasu daga cikin fina-finan sun hada da Gobaran Mata, Kona Gari, Gidan Mara da Uwar Gulma.

Jarumar ta ce duk da cewa ta san al'umma ba su aminta da irin matsayin da ta ke fitowa a fim ba, tana yin hakan don 'fim wani nau'i ne na wayar da kan al'umma.'

A cewarta, duk lokacin da za ta taka wani rawa a fim, bata shakka yinsa amma ta san bata busa hayaki, karuwanci da sauransu domin addininta da al'ada sun hana sai dai tana yi ne fim saboda fadakarwa ga masu yi kuma tana musu addu'a su dena.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Budurwa ta yi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89, ta bayyana dalili

Mafi yawancin mutane za su saka jarumai a wuta idan suna da iko, Hauwa Waraka

Ta kuma ce akasin kallon da wasu ke mata, bata shan miyagun kwayoyi kuma bata damu da abin da mutane ke cewa a kanta ba domin, "Na yi imani da Allah, Manzon Allah, Sunnah, Mala'iku, Rana ta Karshe da Kalmar Shahada."

"Don, na san babu wanda ke da makullin wuta ko aljanna. Domin na san yadda mafi yawan mutane ke kallon mu, idan suna da makullin wuta, mafi yawancin su ba za su kai mu aljanna ba.
"Wasu lokutan idan an ambaci suna na, mutane su kan ce zan tafi wuta. Ina mamakin ko su ne ke da wuta ko aljanna. Amma ban damu ba, na san ko ni wanene da abin da na ke yi, don haka abin da mutane ke fada kaina baya damu na," in ji ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164