Ali Nuhu, Rahama Sadau da sauran jaruman Kannywood sun kauracewa taron karramawa ta 'Zuma'

Ali Nuhu, Rahama Sadau da sauran jaruman Kannywood sun kauracewa taron karramawa ta 'Zuma'

  • Jaruman masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood sun kauracewa taron karrama yan fim na kasa wato 'Zuma Award'
  • Hakan ya kasance ne sakamakon saita taron ya yi daidai da ranar karamar sallah da masu shiryawa suka yi
  • Kungiyar MOPPAN ta yi zargin cewa da gangan suka aikata hakan domin hana musulmai shiga da cin gajiyar taron

Abuja - Manyan jaruman Kannywood irin su Ali Nuhu, Rahama Sadau, Fati Washa, Umar Gombe da sauransu sun goyi bayan hukuncin kungiyar MOPPAN na kauracewa taron karrama yan fim na 'Zuma' da ke gudana a Abuja.

An tattaro cewa ba a ga fuskokin yan Kannywood ba a taron na kasa, duk da cewar wadanda suka shirya taron sun aika masu da katin gayyata.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Ali Nuhu, Rahama Sadau da sauran jaruman Kannywood sun goyi bayan kauracewa taron karramawa ta Zuma
Ali Nuhu, Rahama Sadau da sauran jaruman Kannywood sun goyi bayan kauracewa taron karramawa ta Zuma Hoto: Ali Nuhu Mohammed
Asali: Facebook

MOPPAN, wacce take a matsayin kungiyar hadin gwiwa ta Kannywood, kungiyar shirya fina-finai na arewa (AFMAN) da sauran kungiyoyin shirya fina finan Hausa, ta sanar da hukuncinta na kauracewa taron bisa ikirarin cewa masu shirya taron sun mayar da su saniyar ware.

A cikin wata wasika zuwa ga ministan labarai, Lai Mohammed, MOPPAN da AFMAN, sun bayyana cewa da gangan aka saka taron karramawar ya yi daidai da ranar Sallah domin hana musulmai shiga da cin gajiyar taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumin Kannywood, Umar Gombe, ya bayyana cewa mambobin masana’atar fim din Hausa sun yi biyayya ga shugabanninsu a wajen kauracewa taron na kasa, Daily Trust ta rahoto.

Gombe ya ce:

“A matsayin kungiya, ’yan Kannywood sun bi tsarin shugabancin masana’antar sun yanke shawarar yin biyayya da kauracewa taron. A fili yake cewa a matsayinmu na 'yan kasa, mun cancanci a girmama mu da kuma bamu kulawa. Don haka duk wanda bai shirya yi mana hakan ba, toh yana yiwa kansa ne.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir

Kungiyar fim ta kasa (NFC) tare da hadin gwiwar hukumar birnin tarayya ne suka shirya taron na ZUMA.

Labaran Kannywood: Lilin Baba Yana Daf Da Auren Ummi Rahab

A wani labarin, manuniya tana nuna cewa jarumi kuma mawaki sannan mai daukar nauyin fim din Wuff mai dogon zango ya na gab da auren jarumar da ke haska fim din, Ummi Rahab, Aminiya ta ruwaito.

Akwai labarin soyayyarsu a kwanakin baya wanda hakan ya ja hankalin mutane da dama a ciki da wajen masana’antar.

A makon da ya gabata rade-radin ya karu bayan jarumar ta wallafa hoton Lilin Baba a shafinta na Instagram, inda ta kira shi da “Masoyinta kuma mijinta kuma Aljannarta.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel