Ni nan na bata N40k a fim din Gidan Badamasi, Furodusan Kannywood ya yi martani ga batun Ladin Cimma

Ni nan na bata N40k a fim din Gidan Badamasi, Furodusan Kannywood ya yi martani ga batun Ladin Cimma

  • Nazir Adam Salihi, furodusa a masana’antar Kannywood ya karyata ikirarin da Ladin Cima ta yi na cewar ba a taba biyan ta kudi masu yawa ba a harkar fim
  • Ladin Cima dai ta ce ba a taba biyan ta N50,000 ko N30,000 ko N20,000 ba a fim, hasali ma fim na karshe da ta je, N2,000 aka biya ta
  • Sai dai Salihi ya bayyana cewa shi da kansa ya bata N40,000 a fitowar da tayi a fim din Gidan Badamasi kashi na uku sannan ya sake bata N30,000 a kashi na hudu

Fitaccen furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nazir Adam Salihi, ya magantu a kan ikirarin da Jaruma Ladin Cima ta yi na cewa ba a taba biyanta kudi masu tsoka a harkar fim ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta dage taron gangamin ta a shiyyar Arewa maso Yamma

Salihi wanda ya yi martani ga ikirarin da dattijuwar jarumar ta yi na cewar ba a taba biyanta N50,000 ko N30,000 ko N20,000 ba fim hasalima fitowa ta karshe da tayi N2,000 aka bata, ya ce babu gaskiya a cikin zancenta.

Ni nan na bata N40k a din Gidan Badamasi, Furodusan Kannywood ya yi martani ga batun Ladin Cimma
Ni nan na bata N40k a din Gidan Badamasi, Furodusan Kannywood ya yi martani ga batun Ladin Cimma Hoto: Leadershp/BBC Hausa
Asali: UGC

Furodusan ya ce shi kanshi ya bata N40,000 a cikin fim din Gidan Badamasi mai dogon zango kashi na uku, sannan kuma cewa ya sake bata N30,000 a kashi na hudu, jaridar Aminiya ta rahoto.

Ya rubuta a shafinsa na Facebook:

"Na biya Ladi Cima (tambaya) dubu arba'in a fim din Gidan Badamasi Kashi na uku; na sake biyan ta dubu talatin a Kashi na hudu.
"Haka nan ko wata daya ba a yi ba na sake biyan ta naira dubu talatin a wani dan bidiyo na fadakarwa Kuma a duka ba ta yi fitowa sama da goma ba.

Kara karanta wannan

Batun Ladin Cimma: Jarumin fim ya yi barazanar tona asirin Naziru Sarkin waka, da sauran furodusoshi

"Haka nan mun yi gyaran scene guda Wanda magana kawai ta yi muka biya ta dubu biyar muka Kuma sai mata abinci na dubu kusan hudu a wuni guda.
"Haka Nan a gabanta Hadiza Gabon ta ba ta dubu dari biyu da saba'in kyauta! Amma duk da Haka ka ji halin Dan Adam. Kai jama'a!!"

Har ila yau, a wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook, marubucin Arewa 24, Nasir Nid, ya tabbatar da cewar a kan idon shi an biya Baba Tambaya kudi har N40,000 na fitowa da tayi a shirin fim.

Ya ce:

“Ladin cimma (Tambaya) Tayi mantuwa
“Da zu nake ganin hirar da BBC Hausa sukayi da fitacciyar jaruma Baba Tambaya inda a cikin hirar take cewa tunda take ba ta taba biyanta dubu ashirin ba, na yi murmushi na ce, Baba tayi mantuwa, na yi mata uziri dacewa shekaru idan sukayi yawa akan samu irin wannan matsalar ta mantuwa.

Kara karanta wannan

Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo

“Ba a jima ba sai kuma na ga mutane sun yiwa wasu yan fim caa, akan wannan maganar da Tambaya ta fada, sai naga a dalci ba ne nayi shiru tunda akwai wani abu da na sani sabanin haka.
“Na san cewa naje location din da ake daukar shirin Gidan Badamasi, lokacin daukar zango na uku, na tarar da Baba Tambaya tayi fitowa hudu, Nazir Adam ya biyata Naira dubu Arba’in kudin aikinta, wani tarihi da ya faru a lokacin shine, Baba Tambaya ba ta taba haduwa da Hadiza Gabon ba sai a lokacin, har ta fada mata wata matsala da take ciki, Hadiza Gabon ta bata kyautar kudi Naira Dubu Dari biyu da saba’in a lokacin.
“Abinda ya sa nayi wannan maganar shine, a duk wani abu da zamu mu ringa yiwa juna adalci. Ni dai na yiwa Baba Tambaya (Ladin Cima ) na mantuwa, ni dai na san ko a fitowarta a cikin shirin Kwana Casa’in da Dadin kowa ba kananan kudade muke bata ba.”

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood Ladin Cima: Ban taba samun sama da N5k a harkar fim nan take ba

Jaridar Legit Hausa ta tuntubi Ladin Cima domin jin karin bayani kan ikirarin furudososhi sai jarumar ta ce ita a yanzu haka kwakwalwarta ta juya sakamakon afuwar lamarin don haka ba za ta ce komai ba.

“Ai a yanzu babu wani labari da za ki samu daga bakina saboda kwakwalwayata ta riga ta juya. Wallahi sai dai ayi hakuri don babu wani bayanii, ai bayanin da kuka gani a BBC ai ba wani bane yayi nice nayi, toh mai kuma ake nema a wajena? Babu wani bayani wallahi kwakwalwata ta juya.
“A yanzu haka bana ma gari, na bar Kanon gaba daya ma don ma kada hankalina ya dunga tashi. Saboda abun da ban taba yi bane nayi, a matsayin shekaruna dole ya dame ni.”

Jarumar Kannywood Ladin Cima: Ban taba samun sama da N5k a harkar fim nan take ba

A baya mun kawo cewa Ladin Cima ta ce ta fara harkar fim ne bayan rasuwa mijinta a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon. A cewarta tana da shekaru 18 a zamanin.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

A hira da tayi da sashin Hausa na BBC, jarumar ta ce ta fara dirama ne tun suna zuwa Kaduna domin a lokacin babu yan fim a Kano, inda ta ce ba a biyansu ko sisi a lokacin illa kawai suna aikin ne saboda sha’awarsu ga aikin.

Sai dai kuma, ta ce tsawon lokacin da ta dauka tana fim, ba ta yi fim din da za a dauko N20,000 ko N30,000 ko N50,000 a bata ba inda ta ce ana biyanta daga N2,000 zuwa N5,000 idan ta yi fim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng