Bawan Allah ya yi wa Hadiza Gabon zagin cin mutunci, ta yi masa martani da kyakyawar addu'a

Bawan Allah ya yi wa Hadiza Gabon zagin cin mutunci, ta yi masa martani da kyakyawar addu'a

  • Wani bawan Allah ya yi wa jaruma Hadiza Gabon zagin rashin mutunci inda ya kira ta da karuwa duk don ta ki amsa shi a sakon da ya tura mata a Twitter
  • Ahmad Babayo ya zundumawa Gabon zagi inda ya kira ta da lalatatta, wacce ake zina da ita, mara mutunci kuma kowa ya san karuwa ce
  • Sai dai Hadiza Gabon ta bada mamaki saboda irin addu'ar da ta yi masa na samun salama da soyayya a rayuwarsa duk da cin mutunci da yayi mata

A ranar 14 ga watan Janairu ne wani ma'abocin amffani da kafar sada zumunta ta Twitter mai suna Ahmad Babayo ya yi wa jaruma Hadiza Gabon zagin cin mutunci ta sashin sakon ta, ya kuma ce mata ta tura wa abokan sana'ar ta su ga irin cin mutuncin da yayi mata.

Kara karanta wannan

Kannywood: Isa ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna kan batancin da ta yi masa

Kamar yadda aka gani, Ahmad Babayo ya bukaci Hadiza ta karbe shi a cikin abokan ta na Twitter, ko ta bi shi a shafinsa amma hakan ba ta yuwu ba.

Bawan Allah ya yi wa Hadiza Gabon zagin cin mutunci, ta yi masa martani da kyakyawar addu'a
Bawan Allah ya yi wa Hadiza Gabon zagin cin mutunci, ta yi masa martani da kyakyawar addu'a. Hoto daga @AdizatouGabon
Asali: Twitter

Kamar yadda yace, ita ta fara bin sa a shafinsa na Facebook wanda ake kyautata zaton shafin bogin ta ne ya bibiye shi. A zatonsa ita ce kuma zai samu sakin fuska a Twitter kamar yadda ya ke samu a Facebook, sai ya ga kamar wulakanci ta yi masa a Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ko da Legit.ng ta duba hoton Babayo, ta ga ba karamin yaro ba ne amma zagin da ya yi wa Hadiza irin wanda ko yaro ne ya yi wa dan'uwansa, dole ne a tuhumi tarbiyyarsa.

Sai dai kuma, yadda jarumar ta kwantar da hankalin ta tare da yi masa addu'a, ya dauka hankalin jama'a masu tarin yawa kuma hakan ya ja aka dinga yin tir da al'amarinsa.

Kara karanta wannan

Duk a cikin so ne: Saurayi ya kaftawa budurwarsa mari sannan ya roki ta aureshi

Kamar yadda ya aika mata:

"Ke shegiya karuwa, ni nafi karfin ki ina da mutunci. Ke ko duk duniya an san ke karuwa ce saboda kafin ku fara yin fim sai an yi ta yin zina da ku. Ke ce fa kika turo min da friend request ta Facebook, kuma na karbe ki kuma ki ka rubuta kina neman mijin aure.
"Wa zai aura 'yar drama, mara hankali saboda an yi ta yin zina da ke. Kin ga kuwa babu wanda zai so ya auri karuwa kamar ke a matsayin matarsa kuma ana cewa 'ya'yansa uwarsu da karuwa ce.
"Hadiza na fi karfin ki saboda ni daga gidan mutunci na ke shiyasa ba na ganin Hausa fim, ke kuma lalatacciya ce, karuwa, mazinaciya ce mai saida mutuncin ta. Idan kin isa ki gwada wa 'yan uwan ki 'yan fim wannan cin mutuncin."

Babu bata lokaci jaruma Hadiza Gabon ta wallafa wannan cin mutuncin da yayi mata tare da yin martani da:

Kara karanta wannan

Annabin 'yan Twitter: Wani ya yi da'awar shi Annabin Allah ne, ya shiga hannun hukuma

"Ina maka addu'ar samun salama da soyayya a cikin rayuwar ka."

Bidiyon katafaren Masallacin da Jaruma Hadiza Gabon ta gina saboda Allah

A wani labari na daban, A daren ranar Asabar ne wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram mai suna Kabir Idris Kura ya wallafa bidiyon wani masallaci da aka fara gininsa tun daga tushe har aka kammala shi.

Bawan Allan ya wallafa, "Alhamdulillah, wannan ne masallacin da jaruma Hadiza Gabon ta ginawa bayin Allah domin yin sallah fisabilillah.
"Ginin ya kammala kuma muna mata addu'ar Allah ta'ala yasa mata a mizaninta, ya kuma saka mata da alkhairi, ya ji kan mahaifinta Malam Aliyu Diya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng