Bidiyon katafaren Masallacin da Jaruma Hadiza Gabon ta gina saboda Allah

Bidiyon katafaren Masallacin da Jaruma Hadiza Gabon ta gina saboda Allah

- A daren Ranar Asabar ne wani Kabir Idris Kura ya yi wata wallafa a kan jaruma Hadiza Gabon a Instagram

- Ya sanar da yadda jarumar ta dauka nauyin ginin katafaren masallaci tun daga tushensa har zuwa kammalarsa

- A wallafar, ya sanar da yadda jarumar ta bukaci a sirranta amma ya ce zai fi idan ya bayyana alherin jaruman fim

A daren ranar Asabar ne wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram mai suna Kabir Idris Kura ya wallafa bidiyon wani masallaci da aka fara gininsa tun daga tushe har aka kammala shi.

Bawan Allan ya wallafa, "Alhamdulillah, wannan ne masallacin da jaruma Hadiza Gabon ta ginawa bayin Allah domin yin sallah fisabilillah.

"Ginin ya kammala kuma muna mata addu'ar Allah ta'ala yasa mata a mizaninta, ya kuma saka mata da alkhairi, ya ji kan mahaifinta Malam Aliyu Diya.

Bidiyon katafaren Masallacin da Jaruma Hadiza Gabon ta gina saboda Allah
Bidiyon katafaren Masallacin da Jaruma Hadiza Gabon ta gina saboda Allah. Hoto daga BBC.com
Asali: Instagram

"Ki gafarceni mamana da wannan wallafar. Jama'a da dama sun san sharrin 'yan fim, ya kamata su san alkhairinsu"

KU KARANTA: Zulum ya magantu a kan harin da ake rade-radin 'yan Boko Haram sun kai masa

Alamu na nuna cewa wanda ya wallafa wannan bidiyon dan masana'antar ne domin sunan shafinsa na Instagram yana da alaka da kamfanin shirya fina-finai na two effects.

Haka zalika, alamu na nuna shine mamallakin kamfanin ginin da ya karba kwangilar ginin masallacin.

Hakan ne yasa ya bugi kirji ya nuna wa duniya irin alkhairin 'yan fim duba da yadda suka yi kaurin suna a idon duniya.

KU KARANTA: Sanatan APC ya fusata da ministan ayyuka, ya alakanta kashe-kashe da miyagun tituna

A wani labari na daban, wani dan sanda ya harbi wani saurayi mai suna Olaoye Akintayo, a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, inda take a nan ya rasa ransa. Saurayin ya raka abokansa otal din Ekiti ne, kamar yadda gidan talabijin din Channels suka tabbatar.

Kisan da 'yan sanda suke yi ba tare da kotu ta bayar da izini ba ya kara yawaita ne tun bayan zanga-zangar EndSARS, wanda aka yi don dakatar da cin zarafin da 'yan sanda suke yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng