Masana’antar shirya fina-finai: Jerin jaruman Kannywood 10 da asalinsu ba Hausawa bane
- Masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood na daya daga cikin manyan masana'antu masu muhimmanci a yankin arewacin kasar
- Kannywood ta tara manyan mata da maza daga kabilu daban-daban
- A wannan zauren mun zakulo maku wasu manyan jarumai 10 da asalinsu ba Hausawa bane
Jihar Kano - Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ita ce ta daya a bangaren nishadi a yankin arewacin kasar, kuma ta samu karbuwa sosai a wajen al'umman yankin.
Hakazalika dandalin Kannywood na dauke da manyan jarumai maza da mata wadanda ake ji da su kuma suke taka rawar gani wajen wakiltar al'adun arewa.
Sai dai kuma akwai wasu jaruman da asalinsu ba Hausawa bane amma da wuya mutum ya san da hakan musamman yadda suke magana da tsantsar hausa tamkar yarensu.
A wannan zauren, Legit Hausa ta zakulo maku wasu jarumai 10 da asalinsu ba Hausawa bane.
1. Ummi Zeezee
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ummi Zeezee tsohuwar jarumar masana'antar Kannywood ta kasance asalinta yar Maiduguri ce, iyayenta ba Hausawa bane domin mahaifiyarta yar kabilar Kanuri ce yayin da mahaifinta kuma ya kasance dan Shuwa Arab.
2. Rahama MK
Jaruma Rahama jaruma ce wacce ta saba fitowa a cikin shiri mai dogon zango inda aka fi saninta da Hajiya Rabi Bawa mai kada, ita ma asalinta ba Bahaushiya bace Bayarbiya ce.
3. Maryam Gidado
Shahararriyar jaruma Maryam Gidado wacce aka fi sani da Maryam Babban Yaro itama ba Bahaushiya bace domin asalinta Bafulatana ce kamar yadda ta bayyana a wata hira da aka yi da ita.
4. Hassan Giggs
Fitaccen darakta wanda aka jima ana damawa da shi a masana'antar ta shirya fina-finai, Hassan Giggs shima ba Bahaushe bane, asalinsa Bayarabe ne.
5. Halima Atete
Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13
Halima Atete ma tana daya daga cikin manyan jaruman Kannywood mata da ake damawa da su a yanzu, ta kasance haifarfiyar yar jihar Borno daga kabilar Barebari.
6. Aina'u Ade
Jaruma Aina'u Ade ta shafe tsawon shekaru ana damawa da ita masana'antar ta Kannywood, ita ma kuma asalinta Bayarbiya ce.
7. Amina Amal
Jarumar wacce ta fito a cikin fina-finan masana'antar da dama ta kasance asalinta Bafulatanar kasar Kamaru ce.
Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da ta shigo kasar domin fara harkar fim ko Hausa bata ji. Ta kwashe akalla shekara daya tana koyan Hausa kafin aka fara saka ta a fim.
8. Sani Musa Danja
Jarumi Sani Danja ya kasance tsohon jarumin masana'antar wanda ya ga jiya ya kuma ga yau, sannan da shi a ka kai masana'antar zuwa matsayin da take kai a yanzu.
Ba lallai ne mutum ya fahimci cewa asalin Sani Danja ba Bahaushe bane idan yana Hausa, sai dai kuma asalinsa Bayarabe ne.
9. Maryam Waziri
Tauraruwar jarumar na haskawa a cikin shiri mai dogon zango na tashar arewa 24 wato 'Labarina' haifaffiyar yar garin Gombe ce ta kuma kasance Batangaliya.
10. Mansurah Isa
Mansurah wacce itama ta kasance tsohuwar jaruma a masana'antar shirya fina-finan na Hausa asalinta ba Bahaushiya bace, Bayarbiya ce.
Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri
A wani labarin, mun ji cewa ana tsaka da more shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in sai aka wayi gari da batun auren sirri da wata jarumar fim din ta yi.
Jaridar Dimokardiyya ta ruwaito cewa, Rahama MK, wacce ta fito a matsayin matar Gwamna Bawa Mai Kada ta yi auren ta a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba.
Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba.
Asali: Legit.ng