China Ta Hango Babban Hadari, Ta Tsoma Baki kan Zaman Sulhun Amurka da Iran
- Gwamnatin kasar China ta yi magana kan tashi zaman tattaunawar Islamabad tsakanin Amurka da Iran ba tare da cimma matsaya ba
- Ministan harkokin wajen China, Wangi Yi ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wutar kassahen lokaci ne da ya kamata a yi amfani da shi
- Ya ce China a shirye take wajen taimakawa da ba da gudummuwa don ganin an warware duk wani sabani tsakanin Amurka da Iran
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
China - Kasar China ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran na cikin wani yanayi mai rauni matuka, kuma bai kamata a bari ta rushe ba.
China ta kuma yi kira ga kasashen duniya su tashi tsaye wajen hana duk wani mataki da zai iya jawo sake barkewar yaki tsakanin wadannan kasashe.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa Ministan harkokin wajen China, Wangi Yi, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Mohammad Ishaq Dar.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa burin 'yan Najeriya
Ya ce abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne “kare damar da aka samu na tsagaita wuta” tare da tabbatar da cewa ba ta subuce haka nan ba.
China na goyon bayan kokarin Pakistan
Mista Wangi Yi ya kara da cewa China na maraba da kokari da ma rawar da Pakistan za ta taka wajen warware rikicin Gabas ta Tsakiya gaba daya.
Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin China a shirye take ta bada gudummawa domin samar da zaman lafiya a yankin.
Idan za ku iya tunawa tattaunawar kai tsaye tsakanin Amurka da Iran da ta dauki sama da awanni 12 a birnin Islamabad, ta kare ba tare da cimma yarjejeniya sulhu ta karshe ba.
Hakan ya sa tsagaita wutar da kasashen suka yi na tsawon makonni biyu ta zama ita kadaice katanga tsakanin diflomasiyya da yiwuwar komawa yaki.
Kokarin da Pakistan ke ci gaba da yi
Kasar Pakistan, wadda ta dauki lokaci tana kokarin sasanta Amurka da Iran, ta samu nasarar hada bangarorin biyu a wuri guda a karshen makon da ya wuce, in ji rahoton NBC News.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Sai dai jami’an Pakistan sun amince cewa yanzu an shiga mataki mafi wahala, wato yadda za a dawo da bangarorin kan teburin tattaunawa kafin sabanin da ke tsakaninsu ya rikide zuwa sabon yaki.

Source: Getty Images
Bisa haka ne China ta fito ta bayyana hadarin barin wannan lokaci na tsagaita wuta ya wuce ba tare da sasanta kasashen ba, inda ta ce ta shirya tsaf domin ba da gudummuwa.
Shugaban Amurka ya ja kunnen China
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi China cewa za ta fuskanci manyan matsaloli idan ta aika makamai zuwa Iran.
Trump ya kara da cewa ba shi da damuwa ko za a cimma yarjejeniya da Tehran, yana mai cewa ko da me ya faru, Amurka ce da nasara.
Wannan gargadi da Trump ya yi wa China na zuwa ne bayan fara tattaunawar kasashe uku tsakanin Amurka da Iran da Pakistan a ranar Asabar bayan sanar da tsagaita wuta na makonni biyu.
Asali: Legit.ng