Kasar Iran Ta Gano Matsala a Sharuddan Tsagaita Wuta, Ta Shirya Koya Wa Isra'ila Darasi
- Iran ta dauki zafi kan hare-haren da Isra'ila ta sake kai wa kasar Lebanon bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gabas ta Tsakiya
- Wani jami'i a gwamnatin Iran ya yi gargadin cewa kasar za ta dauki matakin soji matukar ba a tsawatarwa Isra'ila ba
- Majiya ta ce dakatar da fada a kowane bangare, ciki har da yakar kkungiyar gwagwarmayar ta Lebanon, na cikin tsarin tsagaita wuta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin kasar Musulunci ta Iran ta yi barazanar cewa za ta iya ficewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta matukar Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kasar Lebanon.
Iran ta ce za ta janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka idan har Isra'ila ta ci gaba da keta yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare a kasar Lebanon.

Source: Getty Images
Iran ta yi barazanar kai hari Isra'ila

Kara karanta wannan
Bayan cimma matsaya da Iran, sanarwar Shugaba Trump ya raba kan 'yan majalisar Amurka
Wata majiya ce ta bayyana hakan kasa da awanni 24 bayan tsagaita wuta a yakin Amurka/Isra'ila da Iran, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
"Iran za ta fice daga yarjejeniyar idan keta alkawarin tsagaita wuta da gwamnatin yahudawa ke yi ya ci gaba ta hanyar kai hare-hare a Lebanon," in ji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa Tehran na nazarin halin da ake ciki a daidai lokacin da ta bayyana hare-haren da Isra'ila ke kai wa Lebanon a matsayin "ci gaba da keta yarjejeniya."
A cewar majiyar, dakatar da fada a kowane bangare, ciki har da yakar "kungiyar gwagwarmayar Musulunci" ta Lebanon, na cikin tsarin tsagaita wutar da Amurka ta amince da shi.
Yadda Isra'ila ta fara karya alkawari
Sai dai, Isra'ila ta "keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta" tun sanyin safiyar ranar Laraba ta hanyar kaddamar da "munanan hare-hare" a kan Lebanon.
Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa ta kai hari a wurare sama da 100 "cikin mintuna 10" a yankuna daban-daban a Beirut, kwarin Beqaa da kudancin Lebanon.
Hukumomin kasar Lebanon sun bayyana cewa akalla mutane 1,530 ne aka kashe yayin da wasu 4,812 suka jikkata sakamakon hare-haren na Isra'ila.
Iran ta fusata da halayyar Isra'ila
Wani babban jami'i a Iran ya shaida wa kafar yada labarai ta CBS News cewa kasar "za ta hukunta Isra'ila a matsayin martani ga laifin da ta aikata a Lebanon da kuma keta ka'idojin tsagaita wuta".
"Tsagaita wutar ya shafi yankin baki daya, kuma kowa ya san Isra'ila da karya alkawari, don haka harsashi ne kawai zai iya dakatar da ita," in ji jami'in.
Haka zalika wata majiyar soja da ba a bayyana sunanta ba ta kara da cewa Iran na shirin mayar da martani kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra'ila ta yi.

Source: Getty Images
Netanyahu ya fara shirin karya yarjejeniya
A baya, kun ji cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce tsagaita wutar Amurka da Iran ba ta shafi Lebanon ba duk da an ambaci haka a cikin yarjejeniyar.
Ya ce Isra’ila na goyon bayan matakin da Amurka ta dauka na dakatar da hare-hare kan Iran na wucin gadi, amma ya jaddada cewa tsagaita wutar ba ta shafi Lebanon ba.
Netanyahu ya ce Isra’ila na goyon bayan kokarin Shugaban Amurka Donald Trump na tabbatar da cewa Iran ba ta zama barazanar nukiliya da makamai masu linzami ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
