Trump Ya Sako Najeriya a Maganar Sulhu da Iran, Ya Fusata kan Abin da Ya Faru

Trump Ya Sako Najeriya a Maganar Sulhu da Iran, Ya Fusata kan Abin da Ya Faru

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da zargin yada labaran karya dangane da martanin Iran kan tsagaita wuta
  • Trump ya bayyana cewa wani shafin yanar gizo daga Najeriya ne ya kirkiri labarin, yana mai zargin tashar CNN da yada bayanin
  • Shugaban Amurka ya ce an umarci tashar da ta janye rahoton, yana gargadin cewa yada irin wadannan labarai na haifar da hadari ga tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi Najeriya da yada labaran karya dangane da martanin Iran kan sanarwar tsagaita wuta da ya fitar.

Hakan ya biyo bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta har na tsawon makonni biyu tsakanin kasar da Iran a yakin da ake yi.

Trump ya soki Najeriya da yada karya
Shugaba Donald Trump na Amurka da Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na Truth Social inda danganta rahoton da kafar yada labarai ta CNN, yana mai cewa an kirkiri labarin ne gaba daya ba tare da tushe ba.

Kara karanta wannan

Shirin tsagaita wuta tsakanin Iran, Amurka ya kawo gagarumin sauyi a duniya

Donald Trump ya fusata da yada labaran karya

A cewarsa, wani shafin yanar gizo daga Najeriya ne ya fara yada wannan rahoto, yana mai zargin cewa CNN ta dauki bayanin tare da yada shi ba tare da tabbatar da sahihancinsa ba.

Ya ce:

“Ba wanda zai yarda da irin wannan labarin karya da CNN ta wallafa, inda ta yi ikirarin cewa daga manyan jami’an gwamnatin Iran ya fito, alhali ba haka ba ne.”

Trump ya kara da cewa an kirkiri labarin ne domin tayar da hankali a wani lokaci mai matukar muhimmanci da ke bukatar kulawa sosai.

Ya bayyana cewa shafin da ya fara yada labarin daga Najeriya yana daga cikin sababbin kafafen yada labarai masu tayar da rikici, yana mai cewa CNN ta shiga cikin matsala sakamakon yada bayanin.

A cewarsa, yada irin wadannan labarai na karya abu ne mai hadari wanda zai iya janyo matsaloli masu tsanani ga harkokin kasa da kasa, cewar DailyTrust.

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Trump ya kuma ce an umarci CNN da ta janye rahoton, yana mai jaddada cewa dole ne a dauki matakan da suka dace don hana yada bayanan da ba su da gaskiya.

Trump ya zargi Najeriya ya yada labaran karya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Wane gidan jarida Trump ke zargi?

Kalaman Trump sun jawo hankalin duniya kan yanayin kafafen yada labarai na Najeriya, duk da cewa ba a gano wata kafar labarai da aka danganta kai tsaye da rahoton ba.

Ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, babu wata kafar yada labarai ta Najeriya da aka bayyana ko aka tabbatar a hukumance a matsayin tushen bayanin da CNN ta ambata.

Masu nazarin harkokin yada labarai sun ce wannan lamari ya nuna irin kalubalen da ake fuskanta na yada bayanan karya a duniya inda bayanai ke yaduwa cikin sauri ba tare da sahihin tushe ba.

Trump ya yi gagarumar barazana ga Iran

A baya, an ji cewa Shugaba Donald Trump ya gargaɗi Iran cewa zai shafe gaba daya kasar daga doron kasa a daren yau muddin ba ta buɗe mashigar Hormuz ba.

Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta riga ta fara kai hare-hare kan tsibirin Kharg, wanda shi ne babban wurin fitar da man fetur na kasar Iran.

Wannan shi ne karo na huɗu da Trump yake ɗaga wa'adin kai 'mummunan hari Iran,' inda a yanzu ya ce zai shafe kasar da ƙarfe 8:00 na dare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.