Ana Murna An Tsagaita Wuta, Trump Ya Yi Maganar da Za Ta Iya Harzuka Iran

Ana Murna An Tsagaita Wuta, Trump Ya Yi Maganar da Za Ta Iya Harzuka Iran

  • Shugaba Donald Trump ya sanar da sanya harajin kashi 50 kan dukkan kayayyakin kowace ƙasa muddin aka kama ta da sayar wa Iran makamai
  • Trump ya kuma jaddada cewa Amurka ba za ta sake barin Iran ta ci gaba da sarrafa sinadarin Uranium domin haɗa makaman nukiliya ba
  • Ana fargabar cewa wadannan kalamai na Trump na iya tunzura Iran la'akari da cewa ya yi su ne 'yan sa'o'i kadan bayan yarjejeniyar tsagaita wuta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka – Duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya, Shugaba Donald Trump ya buɗe wani sabon shafin yaƙin tattalin arziki.

Shugaban ya gargaɗi abokan hulda da kawayen Iran cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani muddin suka ci gaba da taimaka wa ƙasar Musuluncin ta ɓangaren soja.

Kara karanta wannan

Bayan tsagaita wuta, Trump ya fadi aikin da Amurka za ta yi tare da Iran

Shugaba Donald Trump ya yi barazana ga kawayen Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt via Getty Images
Source: Getty Images

Donald Trump ya yi barazana ga kawayen Iran

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi barazana cewa Amurka za ta sanya harajin 50% ga duk ƙasar da aka samu tana sayar da makaman yaƙi ga Iran.

A cewar Trump, za a sanya harajin ne kan dukkan kayayyakin da kasar ko kasashen da suke shigar da su Amurka, matakin da ya ce zai fara aiki nan take.

Shugaba Trump ya jaddada cewa wannan sabuwar dokar tasa ba za ta yarda da wani nau'i na togaciya ko rangwame ba ga kowace ƙasa, ko da kuwa ƙasar tana da kyakkyawar dangantaka da Amurka.

Ya rubuta cewa:

"Duk ƙasar da ke kai wa Iran makamai, za a sanya wa dukkan kayayyakin da take sayar wa Amurka harajin kashi 50 nan take; ba za mu nuna sani ko sabo ba."

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

Amurka za ta hana Iran sarrafa Uranium

Wannan gargaɗi na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke ƙoƙarin rage ƙarfin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman ta fuskar dakile ta daga ci gaba da sarrafa sinadaran hada nukiliya.

Jim kadan bayan Iran da Amurka sun amince da tsagaita wuta, Aljazeera ta rahoto cewa Trump ya dawo da batun sinadaran hada nukiliya da ke jibge a Tehran.

Trump ya dage cewa ba za a sake barin Iran ta fadada shirinta na sarrafa uranium ba, wanda hakan ya nuna matsayarsa a fili tun ma kafin a hau teburin sulhu a Islamabad ranar Juma'a.

"Amurka na aiki tare da Iran, wadda muke da yakinin ta shirya samar da sauyin shugabancin mai ma'ana. Ba za a sake barin Iran ta fadada shirinta na Uranimun ba, kuma Amurka na aiki da kasar don tono tare da kwashe dukkan duddugar B-2 Bombers, masu nukiliya da aka birne a can karkashin kasa."

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

- Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

Trump ya ce Amurka ba za ta sake barin Iran ta mallaki sinadaran hada nukiliya ba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Aragchi (dama). Hoto: Valentin Flauraud / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Kalaman Trump na iya tunzura Iran

A halin yanzu, kasuwannin duniya na nazarin yadda wannan barazana za ta shafi harkokin kasuwanci, musamman tsakanin ƙasashen da ke da alaƙa da ɓangarorin biyu.

Masu lura da al'amura na ganin cewa muddin Trump ya aiwatar da wannan barazana, to hakan na iya harzuka Iran, kuma har ya iya kawo tasgaro ga sulhun da ake son kullawa.

Har yanzu dai kasar Iran ba ta mayar da martani kan kalaman Trump na kakaba haraji ga abokan kasuwancinta ko na hana ta ci gaba da sarrafa uranium ba.

Trump ya amince da tsagaita wuta da Iran

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya dakatar da dukkan hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu biyo bayan shiga tsakani da ƙasar Pakistan ta yi.

Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta yi aiki ne kawai idan Iran ta buɗe mashigar tekun Hormuz cikin gaggawa kuma ba tare da wata barazana ba.

Farashin ɗanyen mai a duniya ya fara sauka sakamakon wannan mataki da Trump ya dauka, inda man Brent ya sauka zuwa kusan $103.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com