Yakin Iran/Isra'ila: Yawan Asarar da Amurka Ta Yi yayin Yaki a Gabas ta Tsakiya

Yakin Iran/Isra'ila: Yawan Asarar da Amurka Ta Yi yayin Yaki a Gabas ta Tsakiya

  • Gwamnatin Amurka ta yi asarar jiragen yaƙi da dama a rikicin da take yi da Iran wanda aka shafe fiye da wata guda ana yi
  • Rahotanni sun nuna Iran ta harbo wasu jiragen F-15E, yayin da wasu suka faɗi sakamakon kuskure ko hatsari a wurare daban-daban ciki har da Gulf
  • Hotuna da bayanai daga hukumomi sun tabbatar da lalacewar jirage irin su E-3 Sentry da kuma faduwar KC-135 da ya kashe mutane shida a Iraq

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Rahotanni sun bayyana irin barnar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi wa Amurka yayin da ake yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Majiyoyi sun nuna cewa Amurka ta rasa aƙalla jiragen yaƙi tara a rikicin da take yi da Iran, bisa binciken hotuna da bayanai daga hukumomi.

Kara karanta wannan

Halin da mazauna Iran ke ciki bayan sanar da tsagaita wuta tsakanin kasar da Amurka

An gano asarar jiragen yaki da Amurka ta yi a yaki da Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump, Iran Military Media.
Source: Facebook

A ranar 5 ga Afrilun 2026, CBS News ta bayyana cewa Iran ta lalata jiragen F-15E guda biyu da aka tura domin ceto, tare da hotunan hayaƙi.

Amurka ta cimma yarjejeniya da Iran

Bayan shafe fiye da wata daya ana gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Iran, Amurka ta tabbatar da cewa an cimma matsaya kan tsagaita wuta na makonni biyu.

Wannan ya biyo bayan munanan hare-haren da aka kai wa juna tsakanin Iran da Isra'ila mai samun goyon bayan Amurka.

Harin farko da aka kai a birnin Tehran ya yi sanadiyar mutuwar jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaron kasar.

Iran ta lalata jiragen yakin Amurka da dama
Jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Jiragen yakin Amurka da Iran ta lalata

Rahoto ya nuna cewa a ranar 3 ga Afrilun 2026, Iran ta harbo wani jirgin F-15E a tsakiyar ƙasar, yayin da wani A-10 ya faɗi a Gulf.

An ce matukin jirgin A-10 ya samu damar tserewa daga hatsarin, sannan daga baya aka kai masa dauki, aka yi nasarar kubutar da shi.

Kara karanta wannan

Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci

A ranar 29 ga Maris, 2026 hotuna sun nuna lalacewar jirgin E-3 Sentry a wani sansani a Saudiyya bayan rahotannin kai hari daga Iran, cewar rahoton BBC Hausa.

Haka kuma a ranar 12 ga Maris, jirgin KC-135 ya faɗi a Iraq, inda mutane shida suka mutu, amma hukumomi sun ce ba harin abokan gaba ba ne.

A wani lamari daban, jiragen F-15E guda uku sun yi hatsari a Kuwait ranar 2 ga Maris, 2026 inda aka zargi kuskuren hadin gwiwar dakarun ƙawance.

Iran ta kafa sharadin bude mashigar Hormuz

A baya, mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta kafa sharadin bude mashigar Hormuz bayan barazana da Shugaba Donald Trump ya yi mata a kwanakin nan.

Iran ta ce ba za ta bude mashigin Hormuz ba sai an biya diyya saboda barnar yaki da aka yi mata a wannan rikici wanda ya jawo asarar rayuka ga kowane bangare.

Wani jami’i ya ce za a kafa sabon tsarin doka inda za a rika karbar kudin wucewa kafin a sake bude mashigin ruwa domin samun damar zirga-zirga a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.