Abubuwa 10 da Muka Sani kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta tsakanin Amurka da Iran

Abubuwa 10 da Muka Sani kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta tsakanin Amurka da Iran

Tehran – Ba bakon labari ba ne, cewa Shugaba Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran na tsawon makonni biyu daga daren Talata, 7 ga Afrilu, 2026.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wannan sanarwa ta zo ne ƙasa da sa'o'i biyu kafin cikar wa'adin da ya ɗiba na shafe ƙasar Iran daga doron duniya, matakin da duniya ke fargabar zai iya haddasa yaƙin duniya na uku.

Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Aragchi (dama). Hoto: Valentin Flauraud / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran da Amurka sun tsagaita wuta

A shafinsa na Truth Social, Trump ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan tattaunawa da Firayim Minista Shehbaz Sharif da Field Marshal Asim Munir na ƙasar Pakistan.

A halin yanzu, Trump ya bayyana cewa Amurka ta riga ta cimma muhimman manufofinta na soja, don haka tsagaita wutar zai ba jami'an diflomasiyya sararin kammala yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da sanarwa da Amurka ta yarda ta tsagaita wuta da kasar Musulunci

A ɓangaren Iran kuwa, ministan harkokin waje, Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa dakarun ƙasar za su dakatar da duk wani yunƙuri na kariya muddin Amurka ta daina kai mata hare-hare.

Tehran ta riga ta miƙa wa Washington wani daftarin sulhu mai sharuda 10, wanda Trump ya bayyana a matsayin ginshiƙi mai kyau na tattaunawa, kodayake akwai saɓani a fassarar daftarin game da haƙƙin tace sinadarin nukiliya.

Kafar watsa labarai ta The Times of India ta ruwaito wasu muhimman abubuwa 10 da ya kamata a sani game da wannan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma wa tsakanin Iran da Amurka.

Abubuwa 10 game da tsagaita wutar Iran da Amurka

1. Tsagaita wuta na wucin gadi

Wannan yarjejeniya ba ta kawo ƙarshen yaƙi gaba daya ba; ta zama dakatawa ne kawai na tsawon makonni biyu domin ba da damar tattaunawa.

CNN ta ruwaito Majalisar ƙolin tsaron ƙasar Iran ta jaddada cewa:

"Wannan ba yana nufin an kawo ƙarshen yaƙin ba ne; har yanzu yatsanmu yana kan kunamar bindiga, da an ce mana kule, za mu ce cas."

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

2. Bude mashigar Hormuz

Babban sharɗin Amurka shi ne buɗe mashigar tekun Hormuz baki ɗaya. Trump ya bayyana cewa buɗe mashigar cikin aminci shi ne zai tabbatar da ci gaban tattaunawar.

A shafinsa na X, Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bada tabbacin cewa kasarsa za ta bude mashigar Hormuz a tsawon kwanaki 14 na tsagaita wuta.

Iran ta ce za ta daina kai hare-haren kare kai muddin Amurka ta daina farmakarta.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi a Washignton DC. Hoto: Valentin Flauraud / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

3. Sharaɗin Iran kan dakatar da hari

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa dakarunsu za su daina kai hare-haren kariya ne kawai muddin Amurka ta daina kai hare-hare.

4. Tattaunawa a birnin Islamabad

A cikin makonni biyu masu zuwa, jami'an Amurka da na Iran za su haɗu a Islamabad, ƙasar Pakistan, domin tattaunawa. Pakistan ce ta taka rawar gani wajen shawo kan Trump ya dakatar da shirin ruguza Iran a daren jiya, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

5. Daftarin sulhu mai sharuda 10 na Iran

Legit Hausa ta ruwaito cewa, Tehran ta gabatar da wani daftari mai faɗi wanda ya haɗa da daina yaƙi a Iraq, Lebanon, da Yemen, cire takunkumai, da kuma biyan diyar sake gina ƙasar.

Kara karanta wannan

'Kowa sai ya mutu': Trump ya fadi lokacin da zai 'shafe' Iran daga doron duniya

6. Takaddama kan maganar nukiliya

Akwai saɓani a fassarar daftarin Iran; yayin da fassarar Farsi ta ambaci cewa "an amince da hakkin Iran na tace sinadaran nukiliya", sanawar da aka fitar da Turanci ba ta ɗauke da wannan sadarar. Wannan na iya zama babban cikas ga tattaunawar.

7. Hare-hare na ci gaba da faruwa

Duk da sanarwar, rahotanni sun nuna cewa har yanzu ana samun harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka a yankin tekun fasha, inda ƙasashe irin su Qatar ke ƙoƙarin dakile su yau.

8. Amurka na ganin an samu ci gaba

Trump ya bayyana cewa an riga an amince da kusan dukkan mahimman matsalolin da aka daɗe ana takaddama a kansu, kuma yana ganin daftarin Iran zai iya zama hanyar samar da zaman lafiya.

Donald Trump na ganin cewa akwai ci gaba sosai a kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka, Donald Trump lokacin da ya dura filin jirgin Palm Beach da ke Florida a ranar 27 ga Fabrairu, 2026. Hoto: Mandel NGAN / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

9. Matsalar tsarin sojin Iran

Tsarin rarraba ikon sojin Iran na nufin cewa ba lallai ne dukkan dakarun dake filin daga su bi umarnin tsagaita wuta nan take ba, wanda hakan ka iya janyo kuskuren da zai sake rura wutar yaƙin.

Kara karanta wannan

Amurka da Isra'ila sun tsokano fada, sun farmaki muhimmin waje a Iran

10. Akwai sauran rina a kaba

Duk da wannan tsagaita wuta da aka samu, muhimman matsalolin dake haddasa yaƙin, kamar shirin nukiliya da tasirin Iran a yankin, har yanzu suna nan ba tare da an magance su ba.

Wannan na nufin dorewar zaman lafiyar ta rataya ne kan zurfin tattaunawar da za a yi a Islamabad, duba da cewa Trump ya lashi takobin ruguza karfin gwamnatin juyin juya halin Iran.

Isra'ila ta kalubalanci tsagaita wuta

A wani labari, mun ruwaito cewa, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan tsarin tsagaita wuta da Amurka da Isra'ila suka amince da shi.

A cikin sharuda 10 da Iran ta mika wa shugaban Amurka, Donald Trump kuma ya amince da su akwai daina kai hari Lebanon.

Sai dai a yanzu haka, Benjamin Netanyahu ya fito ya ce babu maganar daina kai hari Lebanon a cikin yarjejeniyar da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com