Iran: Amurkawa Sun Bazama a Tituna, Suna Zanga Zangar Neman Tsige Trump

Iran: Amurkawa Sun Bazama a Tituna, Suna Zanga Zangar Neman Tsige Trump

  • Masu zanga-zangar kin yaƙi a Amurka sun ce tsagaita wuta ta makonni biyu da aka yi da Iran ba za ta magance matsalar da suke kuka da ita ba
  • Masu zanga-zangar da suka cika titunan kasar sun zargi shugabansu, Donald Trump da zama barazana ga duniya don haka dole a taka masa birki
  • Masu zanga-zangar sun bukaci a tsige shi daga mulki nan take, sannan a tabbata an ɗauki matakin doka saboda ayyukan da ya yi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Masu zanga-zangar kin yaƙi a ƙasar Amurka sun bayyana cewa dakatar da hare-hare na makonni biyu da Donald Trump ya sanar da Iran ba ta magance wata matsalarsu ba.

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Rahotanni sun nuna cewa masu magana a wani gangami da aka shirya domin adawa da yaƙin sun yi kakkausar suka kan matakin, suna cewa lokaci kaɗai aka ɓata ba tare da an kawo mafita mai ɗorewa ba.

Shugaba Trump ya fara fuskantar kalubale
Shugaban Amurka Donald Trump a wani taro da magoya baya Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Al-Jazeera ta wallafa bidiyon mutanen suna tattaki tare da buga ganguna domin jan hankalin shugabanni game da buƙatar raba Donald Trump da White House.

Masu zanga-zanga sun yi tir da Donald Trump

DC News Now ta wallafa cewa Wasu da suka yi magana a yayin tattakin sun yi zargin cewa Donald Trump ya zama barazana ga duniya da zaman lafiya baki daya.

Wata mai magana, Stephanie Fox, ta ce:

“Ina ganin wannan (tsagaita wuta) ba za ta magance wata matsala ko guda ba. Ya kamata a saka masa ankwa a yanzu, yau da dare. Mu, duniya baki ɗaya, ba za mu iya bari wannan mutum mai hali irin na mahaukata ya ci gaba da riƙe mulki ba.”

Ta ƙara da cewa:

“(Trump) Barazana ne ga mu duka. Makonni biyu ba su da wani tasiri. Dole ne a kawo ƙarshen wannan yanzu, yau da dare. Shugabanninmu su yi ƙarfin halin da za su kawo ƙarshen wannan. Ya kamata a tsige shi daga mulki nan take, yanzu, yau da dare.”

Kara karanta wannan

Raina Musulunci: An zargi Trump da kira sunan Allah a yanayi maras kyau

Wasu Amurkawa na son a tsige Trump

Wani mai zanga-zanga, Hari Kritana, ya bayyana cewa bai yarda da duk wani abin da Donald Trump ke faɗi ba, yana mai zargin sa da yin ƙarya akai-akai.

Amurkawa na zargin Trump na yaudara
Shugaban Amurka Donald Trump yayin gangamin neman zaɓe a baya Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

A cewarsa:

“Yaudara yake yi, kuma yanzu an gano hakan. Shi mutum ne da ke yawan ƙarya, don haka ba za mu iya yarda da abin da ya ce zai yi ko ba zai yi ba. Saboda haka bai cancanci kasancewa a wannan muƙami ba.”

Ya ƙara da cewa:

"Ban ɗauki abin da yake faɗa da muhimmanci ba kuma. Ina ganin wannan ba gaskiya ba ne. Ya kamata a tsige shi daga mulki.”

Kritana ya kuma bayyana cewa ya halarci zanga-zangar ne domin koyar da ‘yarsa muhimmancin kula da halin da duniya ke ciki da kuma fahimtar abubuwan da ke faruwa.

Ƴar majalisa na son a tsige Trump

A baya, mun wallafa cewa yayin da aka samu matsaya kan tsagaita wuta a yakin Iran da Amurka, wata 'yar majalisar kasar, Ilhan Omar ta fara magana kan tsige Donald Trump.

Kara karanta wannan

Iran ta harbo hatsabibin jirgin Amurka daga sama, ya fado kasa ya wargaje

Ta mika bukatar gaggawa ga shugaban majalisar Amurka tana neman a dawo zama domin tattauna batun tsige shi a hukumance bayan ya dade yana yaƙi da Iran.

Hakan na zuwa ne bayan barazanar shafe Iran a doron kasa da Trump ya yi, wanda ya sha suka daga ƙasashen duniya da wasu shugabanni gabanin a tsagaita wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng