Iran Ta Fitar da Sanarwa da Amurka Ta Yarda Ta Tsagaita Wuta da Kasar Musulunci
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa dakarun ƙasar za su dakatar da duk wani harin kare-kai kan Amurka da Isra'ila
- Majalisar ƙolin tsaron ƙasa ta Iran ta bayyana yarjejeniyar a matsayin "nasara ga al'ummar Iran" tare da gargaɗin Amurka kan sake yin wani kuskuren
- Iran ta yi iƙirarin cewa Amurka ta amince da haƙƙinta na tace sinadarin nukiliya a matsayin wani ɓangare na tattaunawar tsagaita wuta da za a yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran – Bayan sanarwar tsagaita buɗe wuta na makonni biyu da Shugaba Donald Trump ya yi, mahukuntan ƙasar Iran sun fitar da jerin sanarwa a yau Laraba, 8 ga Afrilu, 2026, inda suka bayyana matsayarsu game da lamarin.
Yayin da jami'an diflomasiyya ke maganar sulhu, rundunar juyin juya halin Iran ta bayyana yarjejeniyar a matsayin nasara ga dakarunsu.

Source: Getty Images
Matsayar ministan harkokin wajen Iran
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana a shafinsa na X cewa dakarun Iran za su dakatar da kai hare-haren kare-kai muddin Amurka ta daina farmakarsu.
Ya tabbatar da cewa Iran za ta tsara hanyar zirga-zirga cikin aminci ta mashigar tekun Hormuz a kwanaki 14 na tsagaita buɗe wutar.
Araghchi ya ƙara da cewa Tehran tana nazari kan daftarin sulhu mai matakai 15 da Amurka ta miƙa mata, kuma za ta bada amsa nan ba da jimawa ba.
Ya bayyana cewa Washington ta riga ta amince da "cikakken tsarin" daftarin sulhu da Iran ta gabatar, a matsayin ginshikan tattaunawar da za a yi a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan.
Sanarwar majalisar kolin tsaron Iran
Majalisar ƙoli ta tsaron ƙasa ta Iran ta fitar da wata sanarwa mai zafi, inda ta taya ƴan ƙasar murnar abin da ta kira "nasara ta tarihi," a cewar rahoton CNN.
Sanarwar ta ce:
"Muna isar da saƙon farin ciki ga al'ummar Iran cewa an cimma kusan dukkan manufofin yaƙin, kuma jaruman yaƙinku sun jefa maƙiya cikin halin rashin tabbas da kunyar shan kaye."
Duk da amincewa da sulhun, majalisar ta gargaɗi Amurka da cewa:
"Har yanzu yatsanmu yana kan kunamar bindiga, kuma idan maƙiyi ya tafka ɗan ƙaramin kuskure, zai fuskanci martani mai zafi da dukkan ƙarfinmu."
Sharuɗɗan da majalisar ta jaddada sun haɗa da janye dakarun Amurka daga yankin, biyan diyar yaƙi, da kuma wata tabbatacciyar yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Source: Getty Images
Takaddama kan haƙƙin nukiliya
Wani babban abin da ya ɗauki hankali a sanarwar da kafofin yaɗa labaran Iran suka rarraba shi ne iƙirarin cewa Amurka ta amince da haƙƙin Iran na tace sinadarin nukiliya.
Ofishin jakadancin Iran a ƙasar Indiya ma ya wallafa wannan matsaya a shafinsa na X.
Wannan iƙirarin na zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawar za ta fuskanci ƙalubale sosai, domin Amurka ta daɗe tana adawa da haƙƙin Iran na mallakar nukiliya.
Trump ya ayyana tsagaita wuta da Iran
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa ya amince da bukatar tsagaita wuta tsakanin Amurka da kasr Musulunci ta Iran.
Trump ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bayan buƙatar da Firayim Minista Shehbaz Sharif da Field Marshal Asim Munir na ƙasar Pakistan suka gabatar masa.
Babban sharaɗin da Trump ya gindaya na wannan yarjejeniya shi ne dole Iran ta amince da buɗe mashigar tekun Hormuz baki ɗaya, cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng


