Tsagaita Wuta: Jerin Sharuda 10 Masu Tsauri da Kasar Iran Ta Gindaya wa Amurka

Tsagaita Wuta: Jerin Sharuda 10 Masu Tsauri da Kasar Iran Ta Gindaya wa Amurka

Iran – Bayan sanarwar Shugaba Donald Trump na tsagaita buɗe wuta, an samu bayani dalla-dalla kan sharuda 10 da ke kunshe a daftarin sulhun da Tehran ta gabatar wa Amurka.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wannan daftari, mai dauke da sharudda 10, shi ne wanda Trump ya bayyana a matsayin "ginshiƙi mai kyau" na tattaunawa domin kawo ƙarshen yakin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta gabatar da kudurori 10 ga Amurka na sulhu da tsagaita wuta.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei (hagu) da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Anadolu & Win McNamee via Getty Images
Source: Getty Images

Sharuɗan Iran 10 na tsagaita wuta

Iran ta gindaya waɗannan sharuɗan 10 a matsayin sharar fage na daina dukkan wani gumurzu da sojojin Amurka da kawayenta, kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.

Sharuɗan da Iran ta gindaya su ne:

  1. Dole a tsagaita wuta baki ɗaya a ƙasashen Iraq, Lebanon, da Yemen.
  2. Dole Amurka ta daina kai dukkan wani hari kan ƙasar Iran har abada.
  3. Dole a dakatar da dukkan sauran tashe-tashen hankula dake faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.
  4. Iran ta amince za a sake buɗe mashigar tekun Hormuz ga dukkan jiragen ruwa.
  5. Samar da sababbin dokoki da za su tabbatar da ƴancin zirga-zirga da tsaro a mashigar Hormuz.
  6. Dole Amurka ta biya dukkan kuɗaɗen diyya domin sake gina ababen more rayuwa da aka lalata a Iran.
  7. Dole a janye takunkuman tattalin arziki da aka sanya wa Iran baki ɗaya.
  8. Dole a sakar wa Iran dukkan kadarorinta da kuɗaɗenta da Amurka ta toshe.
  9. Iran ta yi alƙawarin cewa ba za ta sake neman mallakar kowane irin makamin nukiliya ba.
  10. Tsagaita buɗe wuta zai fara aiki a dukkan fagen yaƙi nan take idan aka amince da waɗannan sharuɗa.

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Tambayoyin da ake neman amsar su

Rahoton BBC ya nuna cewa akwai tambayoyi birjik da ke bukatar amsa game da sanarwar tsagaita wuta da Donald Trump ya fitar.

Tambayar farko ita ce, shin Trump zai bugi kirji cewa ya ci nasara a yakin, ko dai akwai sauran jan daga? Saboda wasu majiyoyi na cewa zai iya ci gaba da kai hare-haren sama idan wa'adin makonni biyu ya kare, kuma daga bisani ya ayyana cewa ya yi nasara a yakin.

A Gabas ta Tsakiya, tambaya daya mai muhimmanci da ake yi ita ce, shin ya dangantakar Amurka da kawayenta za ta ci gaba da kasancewa?

Uwa uba, ana so a ji ita Isra'ila a wace matsaya ta dauki wannan sanarwa ta Trump? Shin za ta ci gaba da kai hari Iran ko za ta dakata?

Iran ta harba makamai kan Israila

Sai dai kuma, 'yan mintuna kadan bayan Trump ya fitar da sanarwarsa, rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta sanar da cewa ta gano tahowar wasu makamai daga kasar Iran.

Kara karanta wannan

Matakin da gwamnati ta ɗauka kan ɗan Amurka da ke 'tunzura Kiristoci' a Jos

Rundunar IDF ta ce tsarin tsaron kasar na kokarin ganin ya kakkabe makaman da Iran ta harbo masu, yayin da aka kunna kararrawar gargadi don al'umma su nemi wurin buya tun da wuri.

A cikin daftarin sulhu, Iran ta bukaci Amurka ta biya diyyar dukkan barnar da aka yi mata.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi a fadar White House da ke Washington D.C. Hoto: Drew Angerer/Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya sanar da tsagaita wuta

Tun da fari, mun ruwaito cewa,Shugaba Donald Trump ya dakatar da dukkan hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu biyo bayan shiga tsakani da ƙasar Pakistan ta yi.

Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta yi aiki ne kawai idan Iran ta buɗe mashigar tekun Hormuz cikin gaggawa kuma ba tare da wata barazana ba

Rahoton ya nuna cewa farashin ɗanyen mai a duniya ya fara sauka sakamakon wannan mataki da Trump ya dauka, inda man Brent ya sauka zuwa kusan $103.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com