An Samu Kasa 1 da Ta Shawo kan Trump, Amurka Za Ta Tsagaita Wuta a Yaki da Iran
- Shugaba Donald Trump ya dakatar da dukkan hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu biyo bayan shiga tsakani da ƙasar Pakistan ta yi
- Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta yi aiki ne kawai idan Iran ta buɗe mashigar tekun Hormuz cikin gaggawa kuma ba tare da wata barazana ba
- Farashin ɗanyen mai a duniya ya fara sauka sakamakon wannan mataki da Trump ya dauka, inda man Brent ya sauka zuwa kusan $103
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka – A wani sauyi na bazata da ya kauce wa barkewar babban yaƙi, Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa ya amince da bukatar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.
A daren ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2026, 'yan awanni kadan kafin cikar wa'adin kai harin kare dangi kan Iran, Trump ya ce za a tsagaita wuta na tsawon makonni biyu.

Source: Getty Images
Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan buƙatar da Firayim Minista Shehbaz Sharif da Field Marshal Asim Munir na ƙasar Pakistan suka gabatar masa.
Shugaban kasar ya rubuta cewa:
"Na amince zan dakatar da dukan hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu domin ba da sararin kammala yarjejeniyar zaman lafiya."
Babban sharɗin da Trump ya gindaya na wannan yarjejeniya shi ne dole Iran ta amince da buɗe mashigar tekun Hormuz baki ɗaya, cikin gaggawa, kuma ba tare da wata barazana ba.
Wannan mashiga ita ce mabuɗin tattalin arzikin duniya inda kashi ɗaya bisa biyar na man fetur ɗin duniya ke bi ta cikinsa.
Iran ta mika daftarin sulhu ga Amurka
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya Trump ya yi barazanar cewa muddin ba a buɗe mashigar ba kafin ƙarfe 8:00 na daren yau Talata, to zai shafe Iran daga doron duniya, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.
To sai dai kuma, wannan shiga tsakani na Pakistan ya zama silar kauce wa wannan babban hatsari da duniya ke fargabar zai iya jawo yakin duniya na uku.
Duk da cewa har yanzu ba a riga an sanya hannu kan yarjejeniyar ƙarshe ba, Trump ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba.
Ya bayyana cewa Iran ta aiko wa Amurka da wani daftarin zaman lafiya mai bangarori 10, wanda ya kwatanta a matsayin "mataki mai kyau wanda za a iya tattaunawa a kansa."
Trump ya ƙara da cewa:
"An riga an samu matsaya kan kusan dukkan abubuwan da aka daɗe ana takaddama a kansu, amma wannan makonni biyu za su ba da damar kammala yarjejeniyar."

Source: Getty Images
Farashin mai ya fara sauka
Wannan labari na tsagaita buɗe wuta ya kawo sassauci ga kasuwannin duniya, inda farashin danyen mai ya fara sauka a kasuwar duniya, in ji rahoton BBC.
Rahoton ya nuna cewa farashin gangar danyen man Brent ya sauka da kashi 5.8 zuwa $103.42, yayin da ake cinikin man Amurka a kan $103.25, ragin kusan kashi 8.5.
Amurka, Isra'ila sun yi barna a Iran
Tun da fari, mun ruwaito cewa, an shiga firgici a Iran bayan da dakarun Amurka da na Isra’ila suka kaddamar da jerin hare-hare ta sama kan manyan biranen kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa an ji karar tashin bama-bamai da kukan jiragen yaki na sa'o'i da dama a sararin samaniyar birnin Tehran.
Daya daga cikin hare-haren ya shafi shahararriyar jami'ar fasaha ta Sharif (SUT), sannan an ga bakin hayaki na tashi kusa da dandalin Azadi Square.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


